Daily Trust ta samu bayanai a game da yadda gwamnonin jam’iyyar PDP suka raba mukaman shugabanni a majalisar gudanarwa na NWC.
Gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP sun nuna karfinsu a zaben shugabanni na kasa da aka yi, duk da maslaha aka bi wajen fito da sababbin shugabannin.
Gwamnonin da suka taka rawar gani sosai a zaben sun hada da Ahmadu Fintiri, Bala Muhammed, Samuel Ortom, Seyi Makinde da Aminu Tambuwal.
Haka zalika akwai gwamna Nyesom Wike wanda shi ne ya dage a kan tsige Uche Secondus.
Yadda zaben mukaman NWC ya kasance
Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom ya taimaka wajen zaman Iyorchia Ayu shugaban jam’iyya. Sanata Ayu da Ortom sun fito ne daga jiha daya.
An gano Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, ne ya yi ruwa, ya yi tsaki wajen ganin Sanata Samuel Ayanwu ya zama sakataren jam’iyyar PDP na kasa.
Legit