A wani rahoto da aka fitar a News Online, an kawo jerin sunayen daliban wannan aji wanda sai da sunayensu ya ratsa kusan kowane lungu da sako a fadin Najeriya.
Janar Ibrahim Badamasi Babangida
Janar Abdulsalam Abubakar
Janar Mamman Vatsa
Janar Mohammed Magoro
Janar Garba Duba
Janar Gado Nasko
Janar Mohammed Sani Sami
Kanal Sai Bello
Yadda 'yan ajin suka yi fice
A cikin ‘yan wannan aji ne aka yaye Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdulsalam Abubakar wanda duk sun rike kujerar shugaban kasa a mulkin soja.
Mamman Vatsa ya zama Ministan Abuja kamar Mohammed Magoro wanda ya yi Ministan cikin gida. Manjo Janar Gado Nasko da Laftanan Janar Garba Duba, Birgediya Mohammed Sani Sami da Kanal Sani Bello duk sai da suka yi gwamna a wasu jihohin Arewa.
Daga baya Janar Mohammed Sani Sami ya zama Sarkin Zuru. A wannan ajin ne ake da Sarkin Suleja, Auwal Ibrahim da tsofaffin Sarakunan Kontagora da na Lapai. A bangaren shari’a, akwai Idris Legbo Kutigi, Jibrin Ndajiwo da Alkali mai shari’a, Abdullahi Mustapha. James Tsado Kolo, Buba Ahmed, Yunusa Paiko da Abdulraham Gara sun zama Jakadu kamar yadda Jerry Gana da Awaisu Kuta, Ibrahim Tanko suka shiga siyasa.
Yan bokon da aka yi su ne:
Farfesa Musa Abdullahi; Mohammed Dakota; A.I Kolo da M.T. A Suleiman.
Legit
Rubuta ra ayin ka