2023: An samu kungiyar Arewa da ke goyon bayan Tambuwal ya zama Shugaban kasa


Wata kungiyar matasan Arewa tace tsarin karba-karba da ake kira a runguma a zabe mai zuwa na 2023, ba zai tsinanawa Najeriya komai ba.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata, 2 ga watan Nuwamba, 2021, inda aka ji cewa kungiyar Tambuwal Volunteers ta kira taron ‘yan jarida a Abuja.

Shugaban Tambuwal Volunteers, Kwamred Bilal Sidi Abubakar yace mulki ya zagaya Kudu da Arewa, don haka ya dace yanzu a zabi wanda ya dace.

Me ya kamata ayi a zaben 2023?

“An yi aiki da karba-karba tun 1999, kuma duk Kudu da Arewa sun fito da shugaban kasa, amma har yanzu ba mu cigaba ba.”
“Muna bukatar wanda ya cancanta ne ya zama shugaban kasa a 2023, domin an bar kasar nan a baya.” - Bilal Sidi Abubakar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamred Sidi Abubakar ya shaidawa Daily Trust cewa Tambuwal Volunteers, kungiyar matasa ce da aka kafa domin goyon bayan Aminu Waziri Tambuwal.

Wannan kungiya za ta dage wajen ganin gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya fito takarar neman shugaban kasa a 2023, domin ya gyara Najeriya.

Najeriya ta na cikin mawuyacin hali - Sidi Abubakar

Shugaban kungiyar yace kasa ta shiga wani mawuyacin hali da ake bukatar shugaba irin Tambuwal.

“Yan bindiga, masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda sun sa kasarmu a gaba. Ana ta kiran a barka Najeriya ko ta ina.”
“Tattalin arzikin mu ya sukurkuce a gida da waje. Ana fama da yunwa a kasa, kan jama’a ya rabu.” - Bilal Sidi Abubakar.

A jawabinsa, Bilal Sidi Abubakar ya yi kira ga jama’a su gyara kuskuren da aka yi a baya a 2023, yace idan har aka koma gidan jiya, mutane za su kuka da kansu.

Zaben shugabannin PDP

A baya kun ji cewa gwamnoni suka yi abin da suka so a zaben shugabannin PDP, inda har ‘Dan takarar Namadi Sambo ya sha kashi wajen neman mukami a NWC.

Bukola Saraki ya tsira da kujera daya a zaben da aka yi, sannan kuma babu labarin wata kujera da aka ba tsagin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso a PDP.

Source: Legit

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN