2023: Na fasa tsayawa takarar shugaban kasa, Jigon PDP ya yi amai ya lashe bayan nema sau 3


Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, yace a halin yanzun ya daina sha'awar zama shugaban ƙasan Najeriya.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa tun bayan da ya bar ofishin gwamna a 2007, Bafarawa ya nemi tikitin takarar shugaban ƙasa akalla sau uku.

Tsohon gwamnan ya taka takarar shugaban ƙasa karkashin jam'iyyar DPP a zaɓen shekarar 2007, amma ya sha ƙasa a hannun marigayi Umaru Yar'Adua na PDP. 

Bafarawa, ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ACN ranar 21 ga watan Disamba, 2010, kamar yadda dailytrust ta ruwaito. 

Kazalika a shekarar 2019, Attahiru Bafarawa, ya nemi tikitin tsayawa takarar shugaban ƙasa karkashin Inuwar jam'iyyar PDP. Bana sha'awar zama shugaban kasa 

Bafarawa A wata fira da jaridar Punch da aka buga ranar Lahadi, 21 ga watan Nuwamba, tsohon gwamnan Sokoto yace ba zai sake neman wani ofishin siyasa ba. 

Da aka tambayeshi, ta wace hanya zai shawo kan matsalar tsaron Najeriya idan ya zama shugaban ƙasa, Bafarawa yace: 

"An yi rashin sa'a, ba zan zama shugaban ƙasa ba, kuma nima bana son zama shugaban Najeriya." Ko meyasa ya aje kudirinsa na zama shugaban kasa? 

Da yake jawabi kan dalilin ɗaukar wannan matakin, Jigon PDP yace: 

"Wannan tambaya ce ta babu niyyar yin wani Abu, a lokacin da nake siyasa, lokacin ina da niyya, amma yanzun babu kwata-kwata." 

Ina tunanin na yi iyakar bakin kokarina lokacin da na samu dama, hakan da na samu ma ya wadace ni."

 "Saboda haka ba zan sake neman wani mukamin siyasa ba har karshen rayuwata kuma ba zan karbi wani naɗin siyasa ba har karshen rayuwa ta. Amma zan bada shawara idan da bukatar haka." 

Abun kunya ne bayan gwamna ka wuce sanata -Bafarawa

 Tsohon gwamnan yace rashin godiyar Allah ne gwamnan ya nemi zarcewa sanata bayan kammala wa'adin mulkinsa. 

Yace: "Dan me zaka shafe shekaru 8 a kan kujerar gwamnan wata jiha a Najeriya, kuma kace zaka nemi takarar majalisar dattawa?"

 "Bayan ka bada gudummuwa na shekara 8, me zai hana kabar wasu su tafi majalisar ƙasa? 

A matsayin tsohon gwamna, shugaban ƙasaa kaɗai ya kamata ka nema, duk abinda bai kai wannan ba rashin godiya ne da haɗama." 

Legit Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN