Zamu dandana musu zafin da mutane ke ji, Gwamna ya yi barazanar hukunta iyayen yan bindiga


Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi, ya bayyana cewa zai kame iyayen duk wanda aka gano yana da hannu a kashe-kashen dake faruwa kwanan nan a jihar.

The cable ta ruwaito cewa gwamnan ya faɗi haka ne bayan sa hannu a kwantiragin gina hanyar Abakaliki ring, wanda ya gudana a ofishinsa.

Umahi ya ƙara da cewa waɗannan hare-haren da al'umma ke fama da shi ya isa haka, gwamnati ba zata cigaba da lamurta ba.

A cewar wata sanarwa da kakakin gwamnan, Francis Nwaze, ya fitar, Gwamnan yace idan masu aikata wannan kashe-kashen aiki suke bukata, gwamnatin jiha zata samar musu.

Su wa ya kamata a ɗorawa alhakin matsalar?

Bugu da ƙari, gwamnan ya yi gargaɗin cewa idan ya sake jin an tada yamutsi a jihar, sarakunan gargajiya da shugabannin yanki, su zai kama da laifi.

Dailytrust ta ruwaito Umahi yace:

"Bazan sake yarda da kashe-kashe ko ƙona gidaje a jihata ba, idan matsalar miyagun itace rashin aiki, to a kawo mun su, zan samar musu aiki."

"Amma idan suka ƙi amsar wannan tayin, kuma kuka gaza kawo mun sunayensu, to ku abun zai shafa."

"Bayanai kaɗai nake bukata, idan sun amince da wannan tayin, ba zamu kama kowa ba. Zan ɗauke su aiki kuma a canza musu tunani, amma babu wanda zai sake kashe wani."

Wane mataki Umahi zai ɗauka kan dokar zaman gida?

Game da dokar IPOB ta zaman gida duk ranar Litinin, Umahi ya yi kira ga al'umma su fita harkokin kasuwancinsu kamar yadda suka saba, su barwa gwamnati sauran.

Yace:

"Jami'an tsaro zasu fita sintiri ko ina, saboda kunsan yaran nan kuma kunsan iyayensu. Idan aka sake aikata kisa, to zamu fuskanci iyayensu ne."

"Zamu ɗanɗana musu irin ciwon da ake ji, wajen zubar da jinin al'ummar da ba su ji ba basu gani ba."

Source: Legit.ng

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN