Type Here to Get Search Results !

Yau Jirgin da aka kai wa hari na Abuja zuwa Kaduna zai ci gaba da aiki


Hukumar NRC mai kula da jigilar jiragen kasa a Nijeriya ta sanar da ci gaba da aiki a tsakanin Kaduna da Abuja, bayan dakatarda jigilar da ta yi sakamakon wani hari da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kaiwa jiragen har sau biyu. Hukumar ta shaida cewa ta gyara wani waje da harin ya lallata, sannan ta gyara jirgin da aka kaiwa harin.

A jiya Alhamis da safe ne ‘yan bindigar suka binne nakiya a kan layin dogon, inda ya lallata karfen layin dogon, a shekaranjiya Laraba da dare kuma ‘yan ta’addar sun harbi jirgin inda suka fasa tankin gaz din jirgin, sai dai babu rahoton sun raunata matafiya ko masu aikin jirgin.

A sanarwar da hukumar ta bayar ta ce duk wanda ya sayi tikiti a jiya Alhamis ko yau Juma’a, toh ya tuntube sashen kula da abokan cinikin don gyara tikitin don sake amfani da shi a gobe Asabar ko jibi Lahadi. Inda hukumar ta bada shafin intanet kamar haka: customercare@tps.ng ko kuma lambar waya 01 888 7741.

Leadership Hausa

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies