Yau ake cika shekara 10 da yi wa Gaddafi kisan gilla


Shekara goma kenan tun bayan da ƴan tawaye suka kashe tsohon Shugaban Libya Muammar Gaddafi yayin juyin juya halin da aka yi a ƙasar a 2011. Mutane kaɗan a cikin Libya da wasu da ke wajenta sun yi hasashen irin rikici da yaƙin da ƙasar za ta shiga idan Gaddafi ya bar mulkin ƙasar.

Wakiliyar BBC ta Arewacin Afrika Rana Jawad na Libya a lokacin da aka kashe Gaddafi kuma ta yi duba kan irin rikicin da ƙasar ta shiga tun bayan lokacin.

A bayyane, ƴan ƙasar Libya ba su fitowa domin su tuna da ranar mutuwar Kanal Gaddafi. Yadda ƴan tawaye suka yi masa kisar rashin imani a lokacin da ya yi ƙoƙarin guduwa wata alama ce ta wani hali da ƙasar ke shirin faɗawa.

Cikin shekara goman da suka shuɗe, an gudanar da zaɓen ƴan majalisar dokoki har sau biyu, wanda aka yi karo na biyu a 2014 ya ja ƙasar ta dare biyu, inda a ɓangare ɗaya aka samu gwamnati a Benghazi da ke gabashin ƙasar sai kuma a Tripoli da ke yammacin ƙasar.

Yaƙin da masu adawa da juna a ƙasar ke yi ciki da wajen ƙasar ya ƙara raba kan ƙasar. A yau bayan shekarun da Majalisar Ɗinkin Duniya ta shafe tana shiga tsakanin ɓangarorin da ke rikici a ƙasar, da kuma irin matsin lamba da ƙasar ke samu daga sauran ƙasashe, ana sa ran Libyar za ta gudanar da wasu zaɓukan a Disamba mai zuwa - duk da cewa mutane ƙalilan ne ke da yaƙinin zaɓen zai gudana.

Yaƙin basasa da kuma irin ruɗanin da aka shiga na shekaru ba doka a ƙasar, ya sa aka fara mantawa da abin da aka fara tunanin wata sabuwar rayuwa za a shiga mai daɗi bayan juyin juya halin da aka yi.

Sai dai a maimakon haka, farar hula ne suka yi ta gwagwarmaya da rayuwarsu domin su tsira a tsawon waɗannan shekaru.

Amma duk da haka akwai sauran wasu ƴan Libyan da suka ci gaba da hanƙoron ganin lamura sun daidaita tare da samun ƴancin da aka yi zaton za a samu shekara goma da suka wuce bayan hamɓarar da Gaddafi.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN