Yar NYSC da yan bindiga suka sace kan hanyarta na zuwa jihar Kebbi: Alhakin NYSC ne su ceto ta Inji Sanata Shehu Sani


Sanata Shehu Sani ya ce hukumar NYSC ne ke da alhaki kan sace masu yi wa kasa hidima su biyu da yan bindiga suka yi a Zamfara kan hanyarsu ta zuwa jihar Kebbi.

Iorliam Jennifer Awashima da ke a hoto na sama tare da wani dan NYSC Mai suna Joseph, na daga cikin fasinjojin da yan bindiga suka sace lokacin da suka tsayar da motar bus da suke ciki a yankin Zamfara kan hanyarsu ta zuwa jihar Kebbi domin yi wa kasa hidima a NYSC Batch C Stream One orientation course 2021. 

Yayin da yake bayanin ra'ayinsa kan zancen a shafinsa na Facebook, Sanata Shehu Sani ya ce hukumar NYSC ne ke da alhalin nemowa tare da ceto yan NYSC guda biyu da yan bindigan suka sace saboda hukumar ce ta tura su zuwa jihar Kebbi domin su yi hidimar NYSC.

Duba abin da ya ce:

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN