Yanzu yanzu: Jami’an DSS, ‘yan sanda, sojoji sun kewaye kotun Abuja a shari’ar Nnamdi Kanu


Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, an girke jami’an tsaro da yawa a babbar kotun tarayya da ke Abuja don shari’ar Nnamdi Kanu, jagoran kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra ta IPOB.

An ga jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), rundunar sojan Najeriya da jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya suna gadin kowace kofar shiga kotun da titunan da ke shiga ginin kotun.

Ba a bar 'yan jaridar da sunayensu ba sa cikin jerin shirye-shiryen ba a kusa da harabar kotun, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ma'aikatan kotun da suka isa cikin motocin bas an sanya su a layi kuma an bincike su kafin su shiga harabar.

A watan Yuni, an kama Kanu aka kawo shi Najeriya don fuskantar shari'a bayan kejewa beli a 2017.

Kwanan nan gwamnatin tarayya ta sake shigar da sabbin laifukan da ake tuhumar sa da su.

Yanzu haka za a sake gurfanar da shugaban na IPOB din bisa tuhume-tuhume bakwai da laifuka biyar da a baya yake amsa su, wadanda suka hada da aikata cin amanar kasa da ta’addanci.

Legit Hausa

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN