Yanzu yanzu: Duba abin da ke faruwa a kasar Sudan bayan yunkurin juyin mulki


Jagororin sojin Sudan sun kifar da gwamnatin farar hula, sannan suka kama shugabannin siyasa, kana shuka ayyana dokar ta-baci.

Janar Abdel Fattah Burhan, wanda ya jagoranci gwamnatin hadaka da farar hula, ya dora alhakin abin da ke faruwa kan rikicin siyasa na cikin gida.

Firaiministan kasar Abdallah Hamdok, da wasu ministoci hudu na daga cikin wadanda aka yi amanna cewa wasu sojoji sun kama tare da tsare su a safiyar ranar Litinin.

Masu zanga-zanga sun fantsama kan titunan Khartoum, babban birnin kasar kuma wasu rahotanni sun ce an ji karar harbe-harbe.

Tun da farko wata sanarwa daga ma'aikatar yada labaran kasar ta wallafa a shafinta na Facebook cewa wata hadakar rundunar sojojin kasarce ta kama firaiministan da ministoci hudu inda aka tsare da su a wajen da ba a bayyana kawo yanzu.

Rahotanni sun ce an katse layukan sadarwa a kasar.

Har wa yau, an ba da rahoton cafke mai bai wa mista Hamdok shawara kan harkokin yada labarai.

Tuni Kungiyar kwararru a Sudan sun yi kira ga jama'a da su fito kan tituna domin nuna bijirewa juyin mulki.

A ranar Alhamis, dubban 'yan kasar suka cika titunan birnin Khartoum domin nuna goyon baya ga gwamnatin rikon kwarya.

Dakarun Sudan da kuma shugabannin fararen hula a kasar ba sa ga maciji da juna.

Dukkan bangaroirin biyu na cikin gwamnatin hadaka tun shekarar 2019, abin da ke nuna cewa suna share fagen gudanar da zabuka a kasar.

A ranar Alhamis, dubban mutane sun yi zanga zanga a sassan kasar domin nuna goyon baya ga mulkin dimokradiyya.

Kungiyoyin da ke rajin kare dimokradiyya a kasar sun yi kira ga magoya bayansu da su bijirewa duk wani yunkuri na juyin mulki.

Zaman dar dar na karuwa a kasar tun bayan wani yunkurin juyin mulki da aka dakile shi a watan daya wuce wanda aka danganta shi da magoya bayan Mr Bashir.

A farkon watan da muke ciki magoya bayan sojojin gwamnatin hadakar kasar sun bi titunan Khartoum in da suke kira ga sojojin da su karbe ikon kasar.

Tuni aka tura karin sojoji da kuma wasu masu kayan sarki cikin babban birnin kasar, in da aka takaita zirga-zirgar fararen hula.

Kazalika wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, an rufe filin jirgin saman Khartoum a yanzu, sannan an dakatar da saukar jirage daga wasu kasashen.

A ranar Alhamis din data gabata, dubban mutane sun bi titunan kasar inda suka yi zanga-zangar nuna goyon baya ga gwamnatin rikon kwaryar.

Goyon bayan da ake ba wa gwamnatin rikon kwaryar kasar a 'yan watannin baya bayan nan ya jefa tattalin arzikin kasar cikin wani yanayi.

Tun shekarar 1956, Sudan ta gaza samun tsarin siyasa mafi a'a la, sannan kuma ta ke fuskantar yunkurin juyin Mulki.

BBC Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN