Yan sanda sun damke wani mahaifi da ya batar da ɗiyarsa da ya haifa a Adamawa


Jami'an yan sanda a jihar Adamawa sun yi ram da wani mutumi a garin Mayo-Belwa ƙaramar hukumar Belwa, bayan sun gano wata gawa da ake zargin ta ɗiyarsa ce.

Punch ta rahoto cewa mutumin ya yi ikirarin cewa ɗiyar tasa ta ɓata ne a hanyarsu ta komawa gida bayan sun je siyayya a kasuwa.

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje, shine ya tabbatar da cafke mutumin ranar Alhamis.

Kakakin yan sandan yace:

"Wanda ake zargin yana hannun yan sanda, ana cigaba da bincike kan lamarin. Ana zargin mutumin da hannun a ɓatan ɗiyarsa yar shekara 16."

"Ya faɗa mana cewa ya baiwa yarinya kayayyakin abincin da suka siya a kasuwa, ya umarce ta takai su gida."

"A bayanin da ya mana, bayan ya dawo gida ne ya fahimce cewa ɗiyar tasa bata dawo ba. Amma mun gano wata gawa da muke zargin ta yarinyar ce a garin Mayo-Belwa."

Wane hali ake ciki yanzu?

Kakakin yan sandan ya tabbatar da cewa jami'ai zasu tsananta bincike kuma duk wanda aka kama da hannu zai fuskancin doka.

Ɗaya daga cikin mazauna garin Mayo-Belwa, Malam Sahabi Joda, wanda maƙoci ne ga wanda ake zargi, yace lamarin ya faru ne ranar Talata.

Joda ya ƙara da cewa karo na ƙarshe da suka ga wanda ake zargin da ɗiyar tasa shine kwanaki uku da suka gabata.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN