'Yan kasuwa a Kawo ta Kaduna sun yi watsi da umarnin El-Rufai sun koma harkokinsu


Yan kasuwa a Kawo, sun bijirewa umarnin gwamna ta hanyar ci gaba da harkokinsu makonni uku bayan dakatar da kasuwannin mako-mako a wasu kananan hukumomi, ciki har da Kawo a karamar Hukumar Kaduna ta Arewa
.

Daily Trust ta rahoto cewa kasuwar mako-mako na Kawo tana ci a ranar Talata lokacin da aka ziyarce ta, inda ‘yan kasuwa suka ce ba su da wani zabi illa su bijirewa gwamnati tunda ba a ba su wani madadi ba.

Duk da cewa ba a samu fitowar jama'a sosai ba, Abdulaziz Muhammad, wanda ke sayar da hatsi ya ce bai damu ba saboda karin mutane da kwastomomi za su zo daga baya da rana.

A cewarsa:

"Wannan ita ce kasuwa ta mako-mako kawai a kusa da babban birni inda za mu iya siyar da kayanmu da yawa saboda ba a samun riba mai yawa a cikin sauran kwanakin sati.

“Idan ban fito na sayar da abin da nake da shi don ciyar da iyalina ba, gwamnati ba za ta ciyar da ni ba; ba za su ba ni kudi don kula da iyalina ba.

"Akwai bukatar gwamnati ta samar mana da wata hanya. Wannan ita ce sana’ar da na sani kuma na dogara da ita kuma ba ni da wani waje da zan je sai kasuwar Kawo.

A nasa bangaren, Ibrahim Abdullahi, mai sayar da tumatir daga Maraban Jos, ya ce ya bijirewa gargadin abokai da dangi ta hanyar zuwa kasuwa saboda ba shi da zabi.

Idan baku manta ba, mun kawo muku rahoto da muka samo daga Samuel Aruwan cewa, gwamnatin jihar Kaduna ta katse hanyoin sadarwa a wasu sassan jihar tare da hana cin kasuwannin mako-mako a wasu sassan.

Wannan na zuwa ne yayin da lamurran tsaro suka ta'azzara a yankunan Arewa masu yamma, inda 'yan bindiga suka addabi jama'a.

Ba jihar Kaduna kadai ba, an samu jihohin Katsina da Zamfara da suka dauki irin wannan mataki don rage karfi da ayyukan 'yan ta'adda a yankunan.

Legit Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN