Yan bindiga sun sako sarkin Bunguda na Zamfara bayan shafe kwanaki a hannunsu


Kwanaki sama da 30 bayan sace shi, Sarkin Bungudu ta jihar Zamfara, Alhaji Hassan Attahiru, ya sake samun 'yanci daga hannun 'yan bindiga.

A baya mun ruwaito muku cewa, an yi garkuwa da sarkin ne yayin da wasu 'yan bindiga suka dira wa ayarin motocin sa a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar 14 ga watan Satumba.

Rahoton Daily Trust ya ce, wata majiyar tsaro ta ce an saki sarkin ne da yammacin ranar Asabar a jihar Kaduna.

Gazali Shehu Ahmad, wani mai ba da shawara na musamman ga gwamna Bello Matawalle kan dabaru, ya tabbatar da sakin sarkin.

A wani rubutu da ya yi a Facebook, ya rubuta cewa:

"A madadin iyalan Sarki da masarautar Bungudu muna mika sakon godiya zuwa ga al'umma domin addu'a da taimako ta hanyoyi daban daban da suka bayar tun faruwar wannan al'amari har zuwa yau.

"Muna mika godiya zuwa ga gwamnatin jihar Kaduna bisa kokarin da sukayi tayi tun ranar da akayi garkuwa da Sarki har zuwa lokacin daya samu dawowa.

"Muna mika godiya ta musamman zuwa ga gwamnatin jihar Zamfara karkashin shugabancin Hon. Dr. Bello Mohammed (Matawallen Maradun) bisa gagarumin kokarin da tayi domin ganin Sarki yasamu dawowa gida lafiya.

"Muna jinjina zuwa ga hukumar yan' sanda da kungiyar Miyetti Allah bisa kokarin da sukayi na ganin Sarki yadawo gida lafiya.

"Muna rokon al'umma dasu cigaba da yima Sarki addu'a zuwa wasu yan kwanaki nan gaba da zai nemi lafiya da kuma samun natsuwa kafin yadawo ya gana da al'umma.

A baya rahotanni sun bayyana cewa, an sake sarkin Bungudu lokacin da yake tafiya tare da ayarin motocinsa a hanyar Kaduna.

Wannan ba shine karon farko da aka fara sace mai sarauta a yankin Arewa maso yamma ba, an samu da dama a yankin.

Legit Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN