Da duminsa: Yan bindiga da suka sace yar NYSC kan hanyarta na zuwa jihar Kebbi sun bukaci N3m ko su aureta ko su kasheta


Yan bindiga da suka sace yar yi wa kasa hidima NYSC mai suna Iorliam Jennifer Awashima wacce aka sace a Zamfara kan hanyarta na zuwa jihar Kebbi donnyi ya kasa hidima sun ce dole a basu N5m idan ba haka ba za su aureta ko su kasheta. 

Wani dan jarida daga jihar Benue ya sanar da haka a shafinsa na Facebook, kuma ya samar da "screenshot"  na abin da ya ce yan uwan ta ne suka wallafa.  LIB ta ruwaito.

Sakon ya ce yan bindigan sun tuntubi iyayenta inda suka nemi a biyasu N3m kuma suka yi barazanar cewa idan ba a biya su kudin cikin dan karamin lokaci ba za su aureta ko su kashe ta. 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN