Yadda wani mutum ya harbe mutane da kwari da baka, duba yadda ta faru


Aƙalla mutum biyar ne suka mutu, wasu kuma suka samu rauni a Norway bayan wani mutum ya kai musu hari da kwari da baka.

Jami'an ƴan sandan ƙasar sun shaida cewa wannan lamarin ya faru ne a garin Kongsberg da ke arewa maso yammacin Oslo babban birnin ƙasar.

Rahotanni sun ce mutumin ya yi amfani da kwari da bakar inda ya rinƙa saita mutane yana harbinsu a cikin wani katafaren shagon sayar da kayayyaki, daga baya kuma ya bazama cikin gari ya ci gaba da harbin.

Wasu daga cikin hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda kibiyoyin da maharin ya harba suka maƙale a bango.

Bayan kai harin, cikin gaggawa sai ga motocin kwana-kwana sun isa wurin da lamarin ya faru, haka motocin ƴan sanda da jirage masu saukar ungulu sun isa wurin inda suke ta shawagi domin ƙara tabbatar da tsaro.

Shugaban ƴan sandan ƙasar, Oeyvind Aas ya ce an kama wani da ake zargi kuma da alama ya yi gaban kansa ne wajen kai wannan hari ba tare da taimakon kowa ba.

''Dangane da irin bayanan da muke da su a yanzu, mutumin shi kadai ya kai wannan hari, ganin yadda lamarin ya faru, dole ne dama a yi bincike domin ganin ko wannan hari na ta'addanci ne. Ba a yi wa wanda ake zargin tambayoyi ba, don haka ya yi gaggawa tun yanzu a san dalilinsa na kai wannan hari.

Tuni aka hanzarta da waɗanda suka samu rauni zuwa asibitoci mafi kusa.

Rundunar ƴan sandan ƙasar ta bayar da umarni ga duka jami'an yan sandan ƙasar su tabbatar suna ɗauke da bindigogi a tare da su saboda tsaro. Dama ƴan sanda a ƙasar ba su cika yawo da makami a tare da su ba.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN