Wani mutum mai shekara 48 mazauni kauyen Mwathia a mazabar Karumandi da ke gundumar Kirinyaga a kasar Kenya ya haka wa kansa kabari sai ya banka wa gidansa wuta ya kone kurmus daga bisani ya kashe kansa.
Wani ganau ya ce mutumin mai suna Joel Muthike ya banka wa gidansa wuta kuma ya diga amfani da adda yana koran jama'a da suka kawo agaji domin kasahe wutar.
Daga bisani ya kashe dabbobinsa kuma ya juya ya kashe kansa ta hanyar rataye kansa a wata bishiya.