Yadda matasa 3 suka aika saurayi barzahu da gaggawa, duba dalili


Yansandan jihar Ondo sun kama wasu matasa uku sakamakon kashe wani saurayi bisa zargin satar iPhone 6 ranar Laraba 20 ga watan Oktoba..

Wadanda aka kama su ne Felix Sunday da Shomuye Musa da kuma Oluwatobi Michael. Ana zarginsu da yi wa Tunji George duka har ya mutu sakamakon zarginsa da satar wayar hannu iPhone 6.

Wadanda aka kama sun daure Tunji da igiya kuma suka yi ta azabtar da shi a lamba 6 Keke hotel da ke unguwar Iyana Iyesi a garin Ota.

Bayan sun lura cewa ya matukar jikata sakamakon azabtar da shi da suka yi. Sun garzaya da shi zuwa asibiti amma Likitoci suka sanar masu da mutuwarsa.

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN