Yadda dubun wasu masu satar mutane daga tashoshin mota a Najeriya ta cika


Yan sandan Najeriya sun ce sun kama wani gungun masu satar mutane da ke zuwa har tashoshin mota suna kafa tarko ga matafiya.

Ta ce gungun na mutum 9, kasurguman masu satar mutane ne da suka kware wajen sace matafiya a kan manyan tituna da ke fadin yankin arewa maso yamma.

Haka kuma rundunar yan sandan ta ce ta kwato gurneti 11 da bindigogi 11 da motoci guda 15 a hannun gungu-gungu na mutanen da ake zargi da aikata miyagun laifuka.

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce masu satar mutanen wadanda dukkansu matasa ne 'yan tsakanin shekara 22 zuwa 30, sai guda daya mai shekara 45, na karkashin jagorancin wani Bashir Sule, dan shekara 25.

Ta ce an kama gungun ne bayan 'yan sanda sun bankado shirye-shiryensu na gudanar da wata gawurtacciyar satar matafiya a kan titin Kano zuwa Katsina.

Sanarwar da mai magana da yawun 'yan sandan Nijeriya, Frank Mba ya fitar ta ce gungun kan yi amfani da jagoransa Bashir Sule a matsayin direban motar bas, wadda yakan tuka ya je tasha kuma ya debi fasinjoji.

Daga nan sai ya kama hanya har zuwa inda suka tsara, don gamuwa da sauran gungun, wadanda kan far wa matafiyan su yi musu fashi kafin sace su. Daga bisani kuma su tuntubi 'yan uwa da dangin matafiyan su biya fansa kafin su sake su.

Sanarwar ta ce bincike ya kara bankado yadda shugaban gungun a wani lokaci ya shiga motar bas a matsayin fasinja kuma ya ba da bayanai ga abokan aikinsa wadanda ke labe suna jiran isowar motar don su yi garkuwa da mutanen ciki.

'Yan sanda sun ce a duk al'amuran biyu, Bashir Sule yakan kubuta da kyar a hare-haren.

Haka kuma sanarwar ta ce 'yan sanda sun kama wani gungun mutum 11 da ya yi k'aurin suna wajen aikata miyagun laifuka ciki har da sace mutane da fashi da makami da kuma mallaka da sayar da haramtattun makamai. Ta ce gungun wanda ya k'unshi har da mata biyu kan yi amfani da matan ne wajen safarar makamai daga wannan wuri zuwa wancan.

A lokaci guda kuma sanarwar ta ce an kama gungun b'arayin motoci da ke tsallaka iyakar k'asa daga Nijeriya suna fasa-kwaurinsu zuwa Jamhuriyar Nijar da sauran k'asashe mak'wabta. Ta ce ta gano motoci guda 15 a hannun wad'anda ake zargi da kuma na'urorin jagula lissafin fasahar tsaro ta mota don tafiya da ababen hawan da suka sata ba tare da an gane su ba.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN