Yadda dansanda ya yi wa Likita da majinyata duka a cikin Asibiti, duba dalili


An zargi wasu jami'an tsaro da yi wa wata likita da wasu majinyata mugun duka a babban asibitin Maitama da ke Abuja a ranar Alhamis.

Dr. Okpalla Adaeze, daya daga cikin wadanda jami'an tsaron suka nada, ta sanar da Daily Trust cewa wannan cin zarafin aikin wani dan sanda ne da ya zo a duba shi.

Ta ce hakurin sa ya kare ne lokacin da daya daga cikin dakunan suka ki karbarsa, Daily Trust ta ruwaito.

Adaeze ta ce ba ta kula shi ba saboda bangaren kula da marasa lafiyan da suka isa asibitin da farko sun kula da shi.

"Da gaggawa na sanar da su cewa ba su da matsala da ayyukan gaggawa. Na kara da yi musu bayanin cewa tunda an duba shi kuma bai gamsu da hakan ba, ya je wani wuri. Kawai sai ji na yi ya fara duka na," Adaeze tace.

Ta kara da cewa, sai da wasu majinyata suka shiga lamarin kafin ta samu ta gudu, kuma hakan yasa ya mayar da masifarsa kan wasu majinyata biyu.

Adaeze, wacce ta gano sunan daya daga cikin jami'an da Ogochie Kingsley, ta ce daga bisani ya kira abokinsa dan sanda wanda ya isa asibitin da bindigogi biyu.

Da farko abokin ya yi ikirarin shi jami'in DSS ne kuma ya bukaci Kingsley ya nuna masa wadanda suka kai masa farmakin. Ya nuna wasu majinyata 2 saboda ni na boye. Abokin ya yi amfani da kasan bindiga inda ya dinga dukan majinyacin da aka yi wa aiki."

Jamilu Bala Muhammad, daya daga cikin majinyatan da aka duka, ya zage inda ya jibgi dan sandan.

Ya ce 'yan sanda daga ofishinsu na Maitama daga bisani sun shiga lamarin inda suka damke tare da kulle maharan.

"Yayin da muka isa ofishin, wanda ke ikirarin zama jami'in DSS ne ya ce dan sanda ne shi, kuma ya bukaci Kingsley da ya sanar da cewa majinyatan ne suka kai masa farmaki da adda tare da kaca," yace.

Legit Hausa


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN