Yansandan jihar Katsina sun kama wani matashi mai shekara 37 mai suna Abdulkareem Muhammed sakamakon samunsa da lita 32 na man fetur da ya sa a cikin leda kuma ya boye a cikin jaka na matafiya.
Kakakin hukumar yansandan jihar Katsina SP Gambo Isah, ya gabatar wa manema labarai ranar Talata 26 ga watan Oktoba a Shelkwatar yansandan jihar. Ya ce yansanda masu sintiri ne suka kama shi a kan hanyar Katsina zuwa Jibiya.
Ya ce wanda aka kama ya yi shiga irin na matafiya rike da jaka, sai dai bayan yansanda sun gudanar da bincike kayansa ne suka gano cewa ya saka man fetur a cikin laida uku ya boye a cikin jakar matafiya da yake rike da ita.
SP Gambo ya ce yansanda na ci gaba da aiwatar da dokar hana daukan man fetur a cikin laida ko jarka. Ya ce wadanda aka kama da man fetur a gandun daji za su kai wa yan bindiga za a gurfanar da su a gaban Kotu.
Rubuta ra ayin ka