Yadda wani magidanci ya aika matarsa Lahira nan take tare da dan da suka haifa, duba dalili


Rahotanni daga jihar Ebonyi sun bayyana cewa wani mutumi ya sheƙe matarsa mai ƙaunarsa da ɗan da suka haifa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Mutumin ya kuma fita zuwa kan titin anguwar da suke, inda ya jikkata wasu mutum shida da adda.

Mazauna yankin Isiofumini Isieke a Ebonyi inda abun ya faru ranar Talata, sun bayyana cewa sun yi matukar mamaki da abinda mutumin mai suna, Kenneth Nwoha, ya aikata.

A cewarsu, ba tare da tsammani ba Nwoha ya hallaka matarsa da kuma É—ansu mai shekara 6 a duniya, sannan ya fito kan hanya ya jikkata wasu shida.

Shin dama mutumin yana da ciwon hauka ne?

Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa mazauna yajin suna tsoron cewa Mista Nwoha ya samu ciwon taɓin kwakwalwa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A cewar majiyar, yaro É—an kimanin shekara shida, da kuma dattijo É—an shekara 60, suna daga cikin waÉ—anda mutumin ya jikkata a kan layi.

Wane mataki yan sanda suka É—auka?

Rahoto ya nuna cewa lokacin da mutumin ya fito kan titi ya fara farmakan mutane, yan sanda suka kariso kuma suka damke shi.

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Ebonyi, Loveth Odah, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Yace a halin yanzu an kai wanda ake zargin asibiti domin duba lafiyar kwakwalwarsa, yayin da waÉ—anda suka samu raunuka aka duba lafiyarsu.

A wani labarin na daban Yan sanda sun kame waÉ—anda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano

Rundunar yan sanda reshen jihar Kano, ta bayyana cewa ta damke mutum 7 da ake zargin suna da hannu a kisan wani malami a Kano.

Kakakin yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, yace mutanen sun ce, suna zargin shugaban CAN da É“oye wani mai laifi.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN