Wani mutum ya mutu mintuna kaɗan bayan haɗuwa da mahaifinsa a karon farko cikin shekaru 35


An tabbatar da mutuwar wani mutum bayan mintoci kadan da haduwa da mahaifin sa da ya share shekaru 35 ba su hadu ba.

Kamar yadda LIB ta ruwaito, Paul Cowell mai shekaru 56 ya rasa ran sa bayan babur din sa ya gwabza mummunan karo da babbar mota a Isle of Man a ranar 27 ga watan Satumba.

Lance Live ta ruwaito yadda ake zargin rana ce ta hana shi ganin hanya yayin da yake bin wani titi a Mountain Road Guthries.

Diyar matar sa ta ce abin akwai firgitarwa

Diyar matar sa mai shekaru 22, Demi Ramshaw ta bayyana yadda hatsarin ya auku bayan bai wuci mintoci 10 ba da haduwar Paul da mahaifin sa wanda su ka kwashe shekaru 35 ba su hadu ba.

Kamar yadda Ramshaw ta bayyana bisa ruwayar LIB:

Yanzu haka an bude wata kafa wacce za a tattara kudi don a samu a birne shi.

“Karo na farko kenan da yaran sa 2 su ka ga kakan su, sai ya nufi kabarin mahaifiyar sa dake kusa da Mountain Road.

“Ni da masoyi na mun samu yaro wanda kwanan sa 12 kenan, don haka karon farko kenan da ya gan shi. Abin akwai ban tsoro. Ina ganin har yanzu abokiyar zaman sa, Nicola a firgice take don har Isle of Man taje musamman don ta gan shi."

Legit Hausa

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN