Yansanda sun gurfanar da wani mutum dan shekara 29 mai suna Samuel Jecob a gaban Kotun Majistare da ke Badagry a birnin Lagos bayan ya gutsire yatsar wani dansanda da cizo mai suna Sgt Musa Hassan ranar 12 ga watan Oktoba.
Shafin isyaku.com ya ruwaito cewa mai gabatar da Kara na yansanda ASP. Clement Okuiomose ya gaya wa Kotu cewa wanda aka gurfanar ya aikata laifin ne ranar 3 ga watan Oktoba da karfe 11:30 na safe a shiyar Oloko da ke garin Badagry a birnin Lagos.
Kazalika Okuiomose ya gaya wa Kotu cewa wanda aka gurfanar a gaban Kotu ya watsa wa Sgt Musa Hassan man fetur a jikinsa yayin da yake gudanar da aikinsa.
Alkalin Kotun mai suna Mr Fadaunsi Adefioye ya bayar da belin Jecob a kan N200,000 tare da mutum biyu da za su tsaya masa.
Ya dage shari'ar har zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba domin sauraron shari'ar.
Rubuta ra ayin ka