Wanene Barnawi shugaban ISWAP da yadda ya mutu bayan mutuwar Shikau shugaban boko haram


Rundunar sojan Najeriya ta tabbatar da mutuwar Abu Musab al-Barnawi, wanda shi ne shugban ƙungiyar IS na Yammacin Afirka wadda aka fi sani da ISWAP.

"Ya mutu kuma zai ci gaba da kasancewa matacce," a cewar Hafsan Hafsoshin Tsaro Janar Lucky Irabor.

Sai dai Janar Irabor bai bayar da wani ƙarin bayani ba game da mutuwar Barnawi, wadda aka fara ruwaitowa a watan Satumba.

Ƙungiyar ta ISWAP ba ta ce komai ba game da lamarin, wadda ake yi wa kallon ƙungiyar masu iƙirarin jihadi mafi ƙarfi a Najeriya tun bayan mutuwar shugaban Boko Haram Abubakar Shekau a farkon wannan shekarar.

Bayan haka ne kuma mayaƙan Boko Haram ɗin suka dinga miƙa wuya ga ISWAP da kuma sojojin Najeriya.

Wane ne Barnawi?

Ba a da masaniyya kan Barnawi sosai ba, kamar shekarunsa da kamanninsa.

Sunansa na yanka Habib Yusuf, ana tunanin shi ne ɗan wanda ya kafa Kungiyar Boko Haram Muhammad Yusuf na fari.

An riƙa ganinsa a matsayin mai sassaucin ra'ayi, mai watsi da tsattsauran ra'ayin Boko Haram kamar amfani da yara a matsayin ƴan ƙunar baƙin wake da kai wa Musulmi hare-hare.

Bayan rasuwar mahaifinsa a hannun ƴan sanda a 2009, Shekau aka naɗa jagoran ƙungiyar.

Barnawi ya riƙe muƙamin kakakin Boko Haram, amma sun riƙa yawan karawa da Shekau da sauran manyan shugabannin ƙungiyar kuma a 2013 ya sauya sheƙa zuwa ƙungiyar Ansaru - wani ɓangaren aware na Boko Haram da ke da alaƙa da al-Qaeda.

Sai dai duk da bambance-bambancensu, ƙungiyoyin biyu sun yi aiki tare a lokuta da dama.

Don ɗaukaka martabar Boko Haram a idon duniya, Shekau ya haɗa kai da ƙungiyar IS a 2015. A shekarar da ta biyo baya, IS ta naɗa Barnawai sabon shugaban Boko Haram ko "wali", kuma hakan ya janyo rikici a cikin ƙungiyar. Masu sa ido na ganin an samu sauyin shugabancin ne saboda bambancin ra'ayi tsakanin Shekau da shugabancin IS na ƙoli.

Jaridar IS ta al-Nabaata wallafa wata hira da Barnawi a watan Agustan 2016. A hirar, ya bayyana yaƙin ƙungiyar da ƙasashen Afrika ta Yamma a matsayin yaƙi da "masu ridda" da "masu wa'azin addinin Kirista". Ya yi barazana, a matsayinsa na shugaba, bayar da umarnin kashe Kiristoci da sa bom a coci-coci.

Amma a wani sauyi na tsare-tsaren ƙungiyar, ya lashi takobin kawo ƙarshen hare-haren kai mai uwa da wabi a masallatai da kasuwanni.

Ba kowa ne ya yi maraba da sauyin shugabancin ba, kuma Shekau ya zargi Barnawi da kitsa juyin mulki.

A dalilin haka wannan rikicin na cikin gida, masu mara wa IS baya sun shiga ƙungiyar Iswap, wadda Barnawi ke jagoranta, yayin da Shekau ya ci gaba da zama shugaban Boko Haram. Tun daga nan ƙungiyoyin biyu suka zama cikakkun masu hamayya.

Iswap ta sanar da cewa Shekau ya mutu a watan Mayu bayan tserewa daga yaƙi da mayaƙan Iswap - inda ya zaɓi tayar da bom a jikinsa mai makon miƙa wuya.

Iswap ta ce babban jagoran IS na duk duniya Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurashi ya bayar da umarnin jan daga da Shekau, a dajin Sambisa.

A cewar jaridar intanet ta Najeriya ta HumAngle, Barnawi ya sanar da labarin mutuwarsa ne a wani saƙon murya da aka naɗa a watan Yuni inda ya ce Shekau ya aikata "ta'addancin da hankali ma ba zai ɗauka ba."

"Da lokaci ya yi, Allah ya fitar da jaruman sojoji bayan samun umarni daga shugaban muminai," a cewar Barnawi.

A ƙarshen watan, wasu da ake zargi mayaƙan Boko Haram ne sun tabbatar da mutuwar Shekau a wani bidiyo da wasu jaridun Najeriya da masu sa ido suka wallafa.

Haka kuma, IS ta tabbatar da yadda Shekau ya mutu sannan ta bugi ƙirjin cewa "dubban" mayaƙan Boko Haram sun koma ƙungiyar.

Ƙarƙashin shugabancin Barnawi, Iswap ta mamaye wurare a arewacin Najeriya da yankin Chadi a shekarun baya-bayan nan. Kuma tana aiki a ƙasashe masu maƙwabtaka ciki har da Burkina Faso da Chadi da Kamaru da Nijar da Mali.

Ƙungiyar ta ƙwace sansanonin sojoji da dama tare da samun makamai da kayan aiki daga rundunonin soji na yanki. Haraji da take karɓa daga hannun mazauna yankunan ta sama mata kuɗn shiga tare da sa hannunta a sana'o'i kamar kamun kifi.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN