Tap di jan: Karuwai sun lakadawa matar aure dukan tsiya a kan kwastomansu kuma mijinta


Wasu mata masu zaman kansu sun haɗu sun lakaɗawa matar aure dukan tsiya saboda ta zo neman mijinta, wanda kwastoma ne.

Aminiya ta rahoto cewa matar taje neman maigidan nata ne a wani Otal dake tasar mota a Birnin Badun Jihar Oyo, bayan samun labarin yana zuwa. 

Wata majiya a tashar motar, wadda aka ɓoye bayananta saboda wasu dalilai, tace matar Bahaushiya ce kuma mijin nata ma Bahaushe ne. 

Meya kawo faɗa har da duka? Majiyar tace: Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma 

 "Magidancin yana zuwa wurin wata karuwarsa ya kwana, yayin da yake wa matarsa ta sunnah ƙaryar cewa harkokin kasuwanci ne suke hana shi dawowa gida." 

"Da matar taga abin ya yi yawa shine taje har Otal ɗin ta gane wa idonta, domin tana zargin can yake zuwa, kuma daga zuwa ta gan shi ya na kwance a gadon karuwa."

 "Zuwan matarsa yasa karuwar ta faɗa wa kwastoman ya daina zuwa wurinta domin ba ta son wani abu ya haɗa ta da matarshi." Shin ya daina zuwa? Majiyar ta ƙara da cewa magidanci bai daina zuwa kwana wurin wannan mata mai zaman kanta ba, hakan ya sa matar ta dawo a karo na biyu. 

"Da matar da sake dawowa ta yi kokarin cewa wajibi mijinta ya zo su tafi gida kafarta kafar shi amma yace sam ba zai tafi ba." 

"Hakan ya harzuƙa matar, ta fara bugun ɗaya daga cikin karuwan, nan take suƙa taru suka mata dukan tsiya, har sai da aka kaita asibiti." 

Legit
Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE