Tap di jan: Duba bidiyo da hotunan maciji mafi girma da aka taba gani a duniya


Hotuna da bidiyo sun bayyana gagarumin dankararen macijin da ya fi kowanne girma a fadin duniya ana daga shi da mota.

 Dankareren dabban an tsince shi ne yayin da wasu ma'aikata suke gyara tare da kakkabe gandun dajin Dominica, jaridar the-sun news ta US ta wallafa. 

A bidiyon da ya bayyana, mutumin da ke nadar bidiyon cike da mamaki tare da al'ajabi aka ji ya na cewa: "Wayyo mahaifiyata, mene ne wannan? 


Katon macijin wanda a kalla ya fi taku goma a tsayinsa, an gan shi da ran shi kuma an daga shi ne da motar haka manyan ramuka. 

Tun bayan da aka wallafa bidiyon a kafafen sada zumuntar zamani a makon da ya gabata, bidiyon ya ja hankula inda miliyoyin mutane suka dinga kallo cike da mamaki. 

Da yawa daga cikin masu kallo sun nuna mamakinsu kan girman dabban. Wani ya ce: "Wannan ya yi kama da wani irin tarihin duniya." Wani kuwa wallafa yayi ya na cewa: "Tabbas, wannan abun kato ne." 

Har yanzu ba a gane wanne irin maciji ne ya bayyana a bidiyon. Gandun dajin Dominica wuri ne mai fadin mil 29 a tsayi da kuma mil 16 a fadi. Ana kallonsa a tsibirin da ke dauke da yanayi mai kyau domin irin namun daji da ake gani. 

Daya daga cikin irin macijin da ake tsamu a tsibirin shi ne maciji mai matukar hatsari da ake kira da "boa constrictor" wanda ke girma har ya kai kafa 13. A yayin kai farmaki, macijin na cizo da hakoransa kafin daga bisani ya nade mutum ko dabba da jikinsa tare da matse shi har ya mutu, The Sun US ta wallafa. 

Latsa kasa ka kalli bidiyo :

https://mobile.facebook.com/terrese.heronvanta/videos/586405886128019/

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN