Tap di: Duba yadda wani magidanci ya sa maciji ya sari matarshi ta mutu


An yanke wa wani mutum a Indiya hukuncin rai da rai ninki biyu, wanda ba kasafai ake yin irinsa ba, saboda ya hallaka matarsa ta hanyar sa maciji ya sare ta.

Soutik Biswas da Ashraf Padanna ne suka harhada bayanan da suka kai ga kisan gillar matar.

A watan Afrilu na shekarar da ta wuce mijin, wanda ake kira Suraj Kumar mai shekara 28, ya sayi wani maciji (gamsheka) kan dala 92, daya daga cikin macizan da suka fi guba a duniya.

A Indiya ana haramta cinikin maciji, saboda haka Suraj ya yi haramtaccen cinikin daga wani mai kama macizai mai suna Suresh Kumar wanda ke jihar Kerala ta kudancin kasar ta Indiya.

Bayan cinikin ya sanya macijin a wata roba ya tafi da shi gida.

Bayan kwana 13, Suraj ya sanya robar da ya sanya macijin a cikin wata jaka ya tafi gidan surukansa a wani gari da ke da nisan kilomita 44, inda matar tasa Uthra take jinyar wani saran maciji wanda ba a san yadda aka yi ya sare ta ba.

Wani nau'in maciji ne mai tsananin guba wanda ke hallaka dubban mutane a Indiya a duk shekara ya sare ta a kafa lokacin da take gidan mijin.

An yi wa Uthra tiyata har sau uku a kafa a tsawon zaman da ta yi a asibiti na kwana 52.

Masu bincike suka ce a daren ranar 6 ga watan Mayu, Suraj ya bai wa matarsa Uthra ruwan lemo a kofi tare da maganin sa barci.

Shan hadin ke da wuya sai bacci ya dauke ta. Daga nan ne Suraj ya dauko robar da ya sanya macijin, ya zazzage mata shi a ka.

Maciji gamsheka na daya daga cikin macizan da suka fi dafi a duniya

Macijin bai yi mata komai ba sai ya sulale, amma duk da haka Suraj ya sake dauko shi ya jefa mata shi a kanta, tana barcin nan.

Macijin ya kara sauka daga jikinta. A karo na uku ne Suraj ya kama kan macijin ya danna shi a kusa da hannun Uthra na hagu, wanda hakan ya sa macijin ya sare ta har sau biyu. Daga nan sai macijin ya sulale ya je ya hau kan wata kanta da ke dakin ya yi zamansa duk tsawon dare.

''Gansheka ba ta sara sai dai idan an tsokane ta. Suraj ya kama kan macijin ne ya tilasta masa saran matarsa" in ji wani kwararre a kan macizai, Mavish Kumar.

Daga nan sai Suraj ya wanke kofin da ya zuba lemon da maganin sa baccin, ya kakkarya sandar da ya yi amfani da ita wajen tare macijin ya jefar da ita, sannan ya goge duk wasu bayanai na wayarsa da za su sa a gane shi, kamar yadda masu bincike suka ce.

Lokacin da mahaifiyar Uthra ta shiga dakin washegari da safe, kamar yadda ta gaya wa ƴan sanda, sai ta ga ƴarta kwance a gado, bakinta a wage, kuma hannunta na hagu yana reto a gefe daya.

Kuma Suraj shi ma yana cikin dakin in ji ta.

A wannan dakin Uthra ta kwanta saman gado inda aka kashe ta

"Me ya sa ba ka duba ba ko ba barci take ba?" Manimekhala Vijayan ta tambayi mijin ƴar tata.

"Ba na son na dame ta tana bacci," Suraj ya gaya mata.

Daga nan ne iyayenta suka garzaya da ita asibiti inda a can likitoci suka ce rai ya riga ya yi halinsa, amma ta mutu ne sakamakon guba, sai aka kira ƴan sanda.

Binciken da aka yi a kan gawarta ya gano raunuka kanana biyu a kusa da kusa a hannunta na hagu. Kuma jinin da aka diba a jikinta ya nuna cewa a kwai dafin maciji nau'in gamsheka da kuma maganinsa mutum barci.

Dafin gamsheka na iya kashe mutum cikin ƴan sa'o'i ta hanyar dakatar da jijiyoyin numfashinsa.

Bisa korafin da iyayen Uthra suka gabatar ne, ƴan sanda suka kama Suraj ranar 24 ga watan Mayu, dangane da mutuwar matar tasa, mutuwar da suke zargin da hannunsa a ciki.

Bayan bincike na kwana 78 aka tuhume shi da laifuka da aka rubuta a shafi sama da dubu daya, shari'a ta fara.

Sama da mutane 90 ne wadanda suka hada da likitoci da kwararru a kan macizai suka bayar da sheda.

Masu gabatar da kara sun gano kusan dukkanin bayanai da abubuwan da Suraj ya yi amfani da su wajen hallaka matar tasa ciki har da sayen macijin da ya yi na farko wanda ya sare ta watanni kafin ta rasu.

Mai kama maciji, Suresh, wanda Suraj ya sayi macizan a wurinsa, ya amsa cewa shi ya sayar masa da macizan.

Wani kwararre a kan macizai ya gaya wa kotun cewa abu ne mai wuyar gaske a ce maciji nau'in gamsheka ya shiga dakin ma'auratan ta tagarsu da take sama-sama.

An samo macijin mai rai, da mai kama maciji, aka kuma samu mutum-mutumi (kamar matar) aka kwantar a kan gado. Daga nan aka gwada domin a ga ko macijin (gamsheka) zai iya shiga dakin har ya sari mutum, daga nan aka tabbatar ba abu ne mai yuwuwa ba.

Yan sanda sun gano robar da Suraj ya boye macijin da ya kashe matarsa

"Gamsheka ba ta da kuzari da daddare. Duk lokacin da muka saki macijin a kan wannan mutum-mutumin, sai kawai ya sulale kasa ya buya, ko da kuwa mun fusata shi ne ba ya saran mutum-mutumin," in ji mai bincike Mavish Kumar.

Daga nan ne sai ya kama kan macijin ya sa ya sari wani dan tsako da aka daure a jikin mutum-mutumin, inda aka ga raunin saran ya yi daidai da irin wanda aka gani a jikin matar Suraj, Uthra.

A lokacin da alkali M Manoj yake yanke wa Suraj hukuncin zaman gidan yari na rai da rai, a farkon watan nan, ya ce Suraj ya tsara kisan matarsa ta yadda ba za a gane ba, ya yi yadda za a dauka hadarin saran maciji ne.

Masu bincike sun gano cewa saran gamshekar da ya yi sanadin mutuwar, shi ne na uku da Suraj ya yi kokarin kashe matar tasa, Uthra.

A wannan gidan al'amarin ya faru yankin Kollam

Masu bincike sun ce tun bayan haihuwar dansu Dhruv a 2019, Suraj yake ta yin yunkurin da zai kashe matarsa.

Binciken da aka gudanar ya gano irin abubuwan da Suraj ya rika yi a intanet sun danganci neman bayanai a YouTube a kan macizai masu mugun dafi, ciki har da shafin wani fitaccen mai kama maciji na kasar.

Suraj ya kuma gaya wa daya daga cikin abokansu cewa maciji ya kama matarsa a mafarki, ta yadda maciji zai zama sanadin mutuwarta.

Yan sanda sun ce Suraj (tsakiya) ya dade yana kokarin kashe matarsa kusan fiye da shekara

Mahaifin Suraj dan acaba ne da ke tuka babur mai taya uku (keke-Napep), mahifiyarsa kuwa, zaman aure take kawai a gida.

Shekara biyu da ta wuce ya auri Uthra, wadda ya girme ta da shekara uku ta hanyar wani mai dalilin aure.

Ya karbi sadakin zinare mai nauyin giram 768 da mota samfurin Suzuki sedan da kuma tsabar kudi rupee dubu 400 (dala 533). Har ma da alawus na rupee dubu takwas (dala 107) a duk wata na kula da ƴar tasu, wadda ke fama da larurar fahimtar abubuwa cikin sauri.

Masu bincike sun ce Suraj ya fara muzguna wa matar tasa ne domin samun karin kudi daga mahaifanta (babanta dan kasuwa ne da ke sayar da robobi, mahaifiyarta kuwa tsohuwar shugabar makaranta ce da ta yi ritaya), domin ya gyara da fadada gidansa da kuma samun kudin daukar nauyin karatun kanwarsa.

Babban dan sanda mai jagorantar bincike, Apukuttan Ashok, ya ce Suraj ya kuduri aniyar kashe matar tasa ne, ya dauki kudinta ya kuma auri wata matar, abin da ya dade yana tsarawa a tsanake, wanda kuma ya yi nasara a karo na uku.

Lokacin da mai shari'a ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai a makon da ya wuce, kusan Suraj bai nuna wata damuwa ba in ji mai gabatar da kara Mohanraj Gopalakrishnan.

"Wannan wata gagarumar nasara ce a binciken ƴan sanda a Indiya, ind masu gabatar da kara suka iya tabbatar da shedar yadda aka yi amfani da wata dabba wajen kisan kai

Rahotun BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN