Tap di: Duba yadda cikin sa'o'i 8 kacal, Dangote da Bua suka samu karin N30.4b kan dukiyarsu


Arzikin mai kamfanin simintin Dangoten ya karu inda ya kai $13.4 biliyan inda ya cigaba da zama mutum mafi arziki a Najeriya da Afrika.

Kamar yadda kiyasin da ke bibiyar biloniyoyi na Reuters ya bayyana, ya samu karin N1.64 biliyan cikin sa'o'i takwas kacal.

Arzikin Abdulsamad BUA kuwa a daya bangaren ya karu da kashi 1.62 wanda ya kai jimillar dukiyarsa zuwa $4.3 biliyan bayan ya samu karin zunzurutun kudi har N28.85 cikin sa'o'i takwas kamar yadda kiyasin biloniyoyi ya bayyana.

A yayin da dukiyarsa ta kai $13.4 biliyan a ranar Talata, Dagote ya zama mutum na 191 a jerin biloniyoyin duniya, yayin da Abdulsamad ya hau mataki na 574.

Mu sani cewa, Dangote da Abdulsamad suna gasa a masana'antu iri daya insa suke sarrafa siminti, sikari da gishiri. Biloniyoyin 2 a halin yanzu su na hangen masana'antar man fetur ne.

Kano: Ganduje ya aike da Ƙarin N33.8bn kan kasafin kudin 2021 gaban majalisa

A wani labari na daban, Gwamnan Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya aike da karin kasafin kudi har N33.8 biliyan gaban majalisar jihar domin ta amince da shi. Kakakin majalisar, Hamisu Chidari, ya karanta wannan bukatar a zauren majalisar jihar Kano a ranar Talata.

Kamar yadda bukatar gwamnan ta bayyana, N3.22 biliyan zai biyan ma'aikata yayin da N9.2 za a kashe su kan bukatun yau da kullum, sai kuma N21.5 biliyan ta manyan ayyuka, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, da karin kasafin N33 biliyan, jimillar kasafin kudin shekarar 2021 za ta tsaya a N231.7 biliyan.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN