Tana ƙasa tana dabo kan yiwuwar gudanar da babban taron PDP na ƙasa


Ranar Juma'ar nan ne ake sa ran wata kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya da ke zamanta a birnin Fatakwal za ta sanar da hukuncin da ta yanke kan shari'ar da tsohon shugaban jam'iyyar PDP mai adawa wato Uche Secondus ya ɗaukaka, inda yake ƙalubalantar dakatar da shi a matsayin shugaban PDP da aka yi.

Yayin wata ziyara da sashen Hausa na BBC ya kai babban filin taro na Eagle Square da ke Abuja, mun tarar da wuri ya ɗau harami ana ta shirye-shiryen gudanar da zaben duk da rashin tabbacin gudanar da shi.

An sanya tutocin jam'iyyar a dukkanin faɗin filin, baya ga ƙyallaye masu launin fari da ja da kore, ga kuma babban mumbari da aka dirke a tsakiyar filin taron, inda a nan ne za a riƙa kaɗa ƙuri'a da kuma yin jawabi

Mambobin jam'iyyar daga ko ina a fadin Najeriya sun taru a filin tun kafin wannan taro na ranar Asabar, inda suke aikin shirya kujeru da sauran kayayyakin da ake bukata don gudanar da taron.

Shugaban matasa na jam'iyyar PDP ɗin Honarabul SKE Odi Okoye wanda muka tarar a wajen taron da ya je a matsayin sakataren kwamitin shirya bababban taron ya ce ba sa wata fargaba, domina cewarsa jam'iyyarsu na kan doka.

''Za mu ci gaba da ayyukanmu, sai dai in kotu ta yanke hukuncin hanawa, idan hakan ce ta tabbata, to jam'iyya za ta yi ganawar gaggawa domin sanin matakin da za ta ɗauka.

Wasu ƴaƴan jam'iyyar da suka hallara a filin sun ce suna da ƙwarin guiwar cewa taron zai gudana kamar yadda aka tsara, don haka suna nan daram-dam za su kafa su tsare don ganin wannan zaɓe ya gudana.

To shin idan kotu ta ce a fasa zaɓen fa?, tambayar kenan da muka yi wa Aishatu Muhammad Gwani wata ƴar jam'iyyar PDP daga jihar Bauchi, sai ta ce ''Haka za mu haƙura, ai mun saba ganin irin wannan, ba komi a ciki, a kan sa ranar zaɓe ma a daga ai'' inji ta.

Shi dai Uche Secondus na neman kotu ta dakatar da babban taron na ƙasa da babbar jam'iyyar adawar ta tsara gudanarwa ranar Asabar, lamarin da ka iya kawo cikas ga shirye-shiryen da PDP ke yi.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN