Takaddama ta kunno kai tsakanin shugabannin kudu kan wasu mukamai 11 a PDP


Wani rahoto da jaridar The Nation yana nuna cewa wani sabon rikici na kunno kai a jam'iyyar PDP bayan shawarar da shugabannin jam'iyyar suka yanke na mayar da mukamin shugabanta na kasa zuwa Arewacin Najeriya.

An yanke shawarar karkatar da ofishin ne ba tare da fayyace ko tikitin takarar shugaban kasa na 2023 na jam'iyyar zai karkata zuwa kudu ko a bude ga kowa ba.

A cewar rahoton, shugabanni da jiga-jigan PDP na shiyyar kudancin a yanzu sun shiga sabani kan abubuwan da ke faruwa.

Tare da matsayin shugaban jam'iyyar a Arewa, duk sauran mukaman kwamitin aiki na kasa (NWC) na jam'iyyar a halin yanzu a kudanci suma za a ba da su zuwa Arewa.

A bangare guda, duk mukaman da 'yan Arewa ke rike da su a yanzu 'yan kudu za su iya yin takararsu nemansu ne kadai a nan gaba.

Mukamai 11 da ka iya zuwa yankin kudancin Najeriya

Don haka, mukamai 11 na NWC da za su iya zuwa kudu sune:

  1. Mataimakin Shugaban Jam'iyya na kasa
  2. Sakataren Kasa
  3. Shugabar Mata
  4. Sakataren Yada Labarai
  5. Mataimakin Sakatare
  6. Sakataren Kudi
  7. Mai binciken kudi
  8. Mataimakin Ma’aji
  9. Mataimakin Mai ba da Shawara kan harkokin Shari’a
  10. Mataimakin Shugaban Matasa
  11. Mataimakin Sakataren Shirya.

Wata majiyar kuma ta ce a halin yanzu ana takaddama tsakanin shugabannin shiyyoyi uku na yankin kan yadda ya kamata a karkasa mukaman mataimakin shugaban jam'iyya (a kudu) da sakataren kasa.

Yayin da gungun masu ruwa da tsaki na PDP na kudu maso yamma masu biyayya ga Gwamna Seyi Makinde na Oyo ke neman a ba yankin matsayin sakataren kasa, wata kungiya a shiyyar, ta ce tana aiki don tabbatar da cewa Yemi Akinwonmi ya ci gaba da zama a NWC.

Vanguard ta ruwaito cewa kungiyar na samun goyon bayan tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose da Hon. Ladi Adebutu.

Ta hanyar babban taro, kudu maso yamma na iya samun daya daga cikin mukaman biyu.

Amma an tattaro cewa wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar daga ciki da wajen kudu suna goyon bayan tsohon gwamnan jihar Osun, Olagunsoye Oyinlola, kan wannan mukami.

An tattaro cewa watakila kungiyar ta Makinde tana da Eyitayo Jegede daga Ondo da nufin matsayin sakataren kasa, yayin da ake zargin gwamnoni Nyesom Wike da Gwamna Godwin Obaseki ba a shafi daya suke ba kan ra'ayin gwamna Makinde.

Manyan PDP sun amince dan arewa ya shugabanci jam'iyyar

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar PDP a ranar Alhamis 7 ga watan Oktoba ya amince da karkatar da matsayin shugaban jam’iyyar zuwa Arewa.

Hukuncin ya biyo bayan amincewa da shawarwarin da ke kunshe cikin rahoton kwamitin karba-karba na babban taron jam’iyyar PDP na kasa wanda gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi ke jagoranta.

Kwamitin karba-karba na Ugwuanyi ya musanya shugabanci da duk wasu mukamai na zababbun jam’iyyun da mutanen Arewa ke rike da su yanzu da na Kudu.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN