Su Ganduje dai: Duba abin da Gwamna Ganduje ya yi wa Kwankwaso a ranar haihuwarsa a Kano


Mai girma Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya taya tsohon mai gidansa, Rabiu Musa Kwankwaso murnar cika shekara 65 da haihuwa. Abdullahi Umar Ganduje ya aika wa tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso sakon taya murna a jaridar Daily Trust ta ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba, 2021. 

A jiye ne Sanata Rabiu Kwankwaso wanda aka haifa a shekarar 1956 ya cika shekaru 65 a Duniya. A sakon da ya aika wa tsohon Sanatan na jihar Kano, Ganduje ya yaba da irin cigaban da madugun siyasar Kwankwasiyya ya kawo, duk da an raba gari. 

“Godiya ta tabbata ga Allah Madaukaki da ya raya ka da koshin lafiya domin mu sake ganin zagayowar wannan rana ta haihuwarka.” – Abdullahi Ganduje. Abdullahi Ganduje ya yabi abin da ya kira doguwar alakar da ke tsakaninsa da tsohon Ministan tsaron. Bayan aikin ofis, zumunci ya shiga tsakanin ‘yan siyasar. 

Sakon da Abdullahi Umar Ganduje ya aika ya jawo wasu ‘yan siyasar Kano sun fara surutu. Sai dai ba a shekarar nan ne Ganduje ya fara aika irin wannan sako ba. 

Don dole ne - Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda 

Jagororin jam’iyyar APC na Kano irinsu Alhaji Abdulmajid Dan Bilki suna ganin cewa gwamnan ya aika sakon ne domin yana neman inda zai sa kan shi a siyasa. Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda yace gwamna Ganduje ya shiga wani yanayi na gaba kura –baya sayaki, don haka dole ta sa yake kokarin neman kamun kafa. 

Malam Sunusi Bature Dawakin Tofa wanda yana cikin ‘yan tsagin Kwankwasiyya, yace hakan ya nuna Ganduje yana fuskantar barazana ne a rikicin cikin gidan APC. 

Halaccin Alhassan Ado Doguwa

A jiya ake ji cewa Hon. Alhassan Ado Doguwa ya yi wa wadanda yake wakilta ruwan miliyoyin kudi da kayan sana'a. 'Dan majalisar ya kashe har Naira miliyan 70. Tun a shekarar 1999 mutanen Tudun Wada da Doguwa suke zaben Ado Doguwa. Wannan ya sa 'dan siyasar ya yi irin wannan alheri domin ya nuna masu godiyarsa. 

Legit Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN