Shugaban 'yan bindiga, Shehu Rekeb, ya sanar da dalilinsu na kai farmakin Goronyo


Yan bindiga da ke karakaina tsakanin jihohin Sokoto zuwa Zamfara sun dauka alhakin kai farmakin kasuwar Goronyo a jihar Sokoto inda suka halaka rayuka 49 a ranar Lahadin da ta gabata. 

Daya daga cikin gagararrun 'yan bindigan da ke da kusanci da Kachallah Turji da Halilu Sububu, manyan miyagun yankin, mai suna Shehu Rekeb, ya ce sun kai wannan farmakin ne domin daukar fansa kan kisan Fulani da ake yi a yankin. 

A ranar Talatar da ta gabata Daily Trust ta ruwaito cewa, farmakin na hadin guiwa ne saboda yadda sama da babura dari suka tsinkayi kasuwar kuma suka bude wa jama'ar wuta. Sun zagaye dukkan kasuwar tare da budewa masu siye da siyarwa wuta, lamarin da ya kawo mutuwar rayuka arba'in da tara. 

 "Mun ji an kwatanta wadanda suka kai farmakin Goronyo da dabbobi, Mu ba dabbobi ba ne. "Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya fito ya ce hakan. Jama'ar Goronyo sun kashe mutane da yawa, saboda haka ne muka kai musu farmaki tare da kashe su," yace. 

Ya bada misali da yadda aka kashe Fulani Musulmai yayin da suke bauta a Unguwar lalle. Rekeb ya ce, "A lokacin da aka kashe wadannan Fulanin, shugaban kasa bai ce komai ba amma yanzu ya fito ya na martani kan wannan." 

Wani mazaunin yankin a ranar Litinin ya sanar da Daily Trust cewa, "wannan farmakin Goronyo ba zai rasa alaka da harin daukar fansa ba kan 'Yan Sa Kai' saboda kashe makiyaya 11 da suka yi a kasuwar Mamande da ke karamar hukumar Gwadabawa ta jihar. “Wadannan mutanen na kamawa tare da kashe Fulani babu dalili," yace. 

Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN