SERAP: Dole Gwamnatin Buhari ta dakatar da batun bibiyar sakonnin yan Najeriya a shafukan sada zumunta


Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta shigar da gwamnatin Najeriya ƙara, inda ta buƙaci kotu ta dakatar da yunƙurinta na bibiyar saƙonnin 'yan ƙasar a shafukan sada zumunta irinsu Whatsapp.

Ƙungiyar ta ce matakin warewa hukumomin tsaro wani kaso a cikin kasafin kuɗi don satar karanta saƙonnin 'yan ƙasa, abu ne da ya saɓa wa tsarin mulkin Najeriya, wanda ya ba su damar samun kariyar bayanansu da kuma 'yancin faɗar albarkacin baki.

Ba wannan ne karon farko da masu fafutuka a Najeriya ciki har da SERAP ke takun saƙa da hukumomi kan abin da ya shafi 'yancin faɗar albarkacin baki ba.

Sai dai zargin satar karanta saƙonnin 'yan ƙasar a shafukan sada zumunta a ganin SERAP wuce gona da iri ne.

Kuma hakan ya sa ƙungiyar maka Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a kotu bisa zargin ware biliyoyin naira ga hukumomin tsaro, don mallakar wata manhaja da za ta ba su damar sanin wainar da 'yan kasar ke toyawa a shafukansu na sada zumunta kamar Whatsapp.

Kungiyar SERAP ta ce bukatarta a yanzu ita ce kotu ta taka wa shugaban Najeriyar burki kan wannan yunkuri da suke gani ƙarara ya saɓa doka.Najeriya dai na fama da ɗumbin matsalolin tsaro a wannan lokaci kama daga hare-haren 'yan fashin daji da kuma rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya da ya shafe sama da shekara 12, a don haka ake gani ba bu mamaki matakin na gwamnatin kasar na da alaƙa da sha'anin tsaro.

To sai dai kuma wata majiya da ba ta yar da a ambace ta a gwamnatin Najeriya, ta ce hukumar kula da harkokin sadarwa ta ƙasar wato NCC, ba ta da masaniya ballantana hannu a wannan batu, kuma ba huruminta ba ne bibiyar saƙonnin 'yan kasa, don kuwa ita tana hulda ne da kamfanonin sadarwa amma ba ɗaiɗaikun mutane ba.

Hukumomin Najeriya dai sun ce zuwa yanzu ba su samu wani sammacin kotu a kan wannan ƙara ta SERAP ba.A baya ma dai, ƙungiyar SERAP din ta shigar da gwamnatin Najeriya ƙara kan matakinta na rufe shafin sada zumunta na Twitter, tun a farkon watan Yuni.

Wata ƙididdigar kamfanin Facebook ta nuna cewa akwai mutum miliyan 33 da ke amfani da whatsapp a Najeriya.

Shafin sada zumunta na whatsapp, manhaja ce da ke bugun ƙirji da fasahar kare sirri tsakanin masu amfani da shafin, sai dai masana harkokin fasahar sadarwa sun ce ana iya amfani da wasu manhajojin leƙen asiri wajen keta iyakokin whatsapp don satar sauraro ko karanta saƙonni.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN