Na ranste da Al-Qur'ani ba zan nemi tazarce ba, Shugaba Buhari


Shugaba Muhammadu Buhari ya rantse da Al-Qur'ani mai girma cewa wa'adinsa na karewa ba zai nemi ya yi tazarce kan kujerar mulkin Najeriya ba. Buhari ya bayyana haka ne a ganawar da yayi da wasu yan Najeriya mazauna Kasar Saudiyya yayinda yake shirin bankwana da kasar. 

Mai magana da yawun shugaban kasan, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a. Shugaban kasar ya bada tabbacin cewa wa'adinsa na karewa zai sauka daga mulki. 

Yace: "Na rantse da Al-Qur'ani mai tsarki cewa zanyi mulki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada kuma zan tafi idan wa'adi na ya kare." Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng! "Babu Tazarce. Bana son wani ya rika magana akan tazarce. Ba zan yarda da hakan ba." 

Cikin dan lokaci na da ya rage zan taimakawa rayuwar yan Najeriya Shugaban kasan ya bayyana cewa cikin dan lokacin da ya rage masa, zaiyi kokari wajen inganta rayuwar yan Najeriya. "Cikin watanni 18 da suka rage na wa'adi na, zan yi duk abinda zan iya na inganta rayukan yan Najeriya, zan yi ne don bauta ga kasar," yace. 

Source: Legit 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN