Matar aure ta kashe mijinta da suka shekara 35 tare, ta ce ta kare kanta ne


Yan sanda a jihar Rivers, a ranar Alhamis sun ce sun kama wata mata mai shekaru 51, Gladys Amadi, daga Chokocho a karamar hukumar Etche a jihar kan kashe mijinta, Napoleon Amadi, da adda. 

Kakakin yan sandan jihar, Nnamdi Omoni, ne ya sanar da hakan yayin holen wacce ake zargin gaban manema labarai a ofishin CID, Port Harcourt, babban birnin jihar, rahoton The Punch. 

Jaridar Vanguard ta rahoto Omoni ya ce, an kama Gladys ne a ranar 8 ga watan Oktoban 2021 kuma ta amsa cewa ta aikata laifin. 

Ya ce: "Bincike ne kan kisan wani Napoleon Amadi. Yan sanda sun tashi sun fara bincike. "Binciken ya yi sanadin kama wata mata da wasu. Bayan zurfafa bincike, ta amsa cewa ita ta kashe mijinta; sun yi rikici ne sai da yamma ya fito da adda zai yanke ta amma ta kwace ta kashe shi da shi. 

"Ta sare shi a wuri da dama a goshinsa, hakan ya yi sanadin mutuwarsa." Kakakin yan sandan ya ce bincike ya nuna Gladys ta wanke jinin bayan halaka mijin don boye abin da ya faru 

Legit Hausa

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN