Kungiyar mawakan APC a jihar Kebbi ta sanar da tsige shugabanta Bello Aljannare, duba dalili


Kungiyar mawakan jam'iyar APC na jihar Kebbi, Kebbi state APC musicians forum, ta tsige shugabanta Bello Aljannare daga mukamin shugabancin kungiyar.

Hakan ya biyo bayan sa hannun Musa Suleiman Sakataren kungiyar a wata takarda da aka raba wa manema labarai, ya ce kungiyar ta tsige Bello Aljannare nan take bayan kammala wani zaman taron da manbobinta suka yi a garin Birnin kebbi ranar Juma'a 15 ga watan Oktoba.

Yunkurin mu na jin ta bakin Bello Aljannare ta wayar salula ya ci tura, domin dai bai amsa kiraye-kirayen da wakilinmu ya yi masa ba. 


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN