Kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani "Arewa Media Writers" ta ziyarci wani shahararren marubuci kuma dan Jaridar mai shafin labarai na Isyaku.com " a garin Birnin Kebbi.
Daga Kungiyar "Arewa Media Writers"
Kungiyar Marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani "Arewa Media Writers" reshen Jahar Kebbi ta ziyarci wani sananne akan harakar Rubutu kuma dan Jarida wato "isyaku Garba zuru" Mamallakin shafin labarau na isyaku.com.
A yayin ziyarar, kungiyar ta tattauna muhimman batutuwa da suka shafi wannan kungiyar, da kuma abubuwan da suka shafi harkar Media,da yanda ya kamata a yi rubutu da kuma taka tsantsan a kan rubutun karya wanda baya da tushe.
Shugaban gidan Jaridar Isyaku.com ya yabawa kungiyar "Arewa Media Writers" sannan ya sha alwashin bada tashi gudummuwa ga wannan kungiya ta hanyar basu horo a kan yanda zasu dauko rahoto da kuma yanda za su yi rubutu a kyauta, da kuma sauran abubuwan da suka shafi kungiya.
Wadanda suka samu damar halartar wannan ziyarar sun hada da:
1. Abubakar Umar G/gaji
State Chairman (AMW)
2. Muhammad Abdulmumini Fana
Secretary General
3. Ibrahim Adamu
Asst Org Secretary
4. Yusha'u Muhammad Nata'ala
Financial Secretary
5. Ibrahim Muhammad
Member.
Abubakar Umar Gwadangaji.
Daga:
Chairman "Arewa Media Writers" reshen jihar Kebbi.