Kotun sharia ta umurci a yi wa magidanci bulala 80 saboda yi wa matarsa ƙazafi kan haihuwar ɗansu na 6


Wata kotun shari'a da ke zamanta a Magajin Gari, Jihar Kaduna, a ranar Laraba ta bada umurnin a yi wa wani treda mazaunin Bakin Dogo, Abdulhamid Yakubu bulala 80.

Kotun ta yanke wannan hukuncin ne saboda Yakubu ya musanta cewa shine mahaifin dansu na shida da matarsa ta haifa kamar yadda NewsWireNGR ta ruwaito.

A cewar ruwaiyar jaridar NewsWireNGR, Alkalin kotun, Murtala Nasir, ya tabbatar da cewa dan da aka haifa na Yakubu ne.

Nasir ya umurce shi ya cigaba da daukan dawainiyar dukkan yaransa shida.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, ta ruwaito cewa a watan Satumba, Yakubu ya maka matarsa Maryam Muhammad a kotu, yana zargin cewa ta ci amanarsa na aure kuma cikin da ta ke dauke da shi ba nasa bane.

NAN ta kuma ruwaito cewa an bawa wanda ya yi karar zabin yin rantsuwa kan cewa ba shine mahaifin dan ta matarsa ta haifa ba ko ya kawo shaida da ke nuna dan ba nasa bane amma ya ki yin hakan.

Ma'auratan sun shafe shekaru 21 suna zaman aure kuma Maryam Muhammad ta haifi dansu na shida da aka saka wa suna Abdulazeez.

A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu

Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN