Karin bayani: Kusan kwana 30 da sace Sarkin Bungudu, har yanzu babu labarin inda yake


‘Yanuwa, talakawa da abokan arziki sun shiga wani yanayi tun bayan da ‘yan bindiga suka dauke Sarkin Bungudu, Mai martaba Hassan Attahiru.

Premium Times tace ana neman a cika wata daya da sace Mai martaba Hassan Attahiru a hanyar Abuja, amma har yanzu jami’an tsaro ba su iya ceto shi ba.

A wata hira da aka yi da Sakataren masarautar Bungudu, Usman Ibrahim ya shaida wa BBC Hausa har yanzu ba su ji wani labari game da Mai martaba ba.

“A lokacin da aka dauke shi, mutanenmu da ke wajen jihar suna magana da wadanda suka yi garkuwa da shi. Mun yi tunanin za su fito da shi.”

“Mutanenmu sun fada mana cewa an tabbatar masu da cewa (Sarki) ya na raye.” – Ibrahim.

Alhaji Hassan Attahiru shi ne Sarkin Fulanin Bungudu, kuma ya rike Sakataren gwamnatin jihar Zamfara.

Me na-kusa da Sarki suke cewa?

Wani na-kusa da Sarkin ya sanar da manema labarai cewa ba su san ko Mai martaban yana raye, ko an kashe shi ba, yace an dai yi masu alkawarin fito da shi.

“Babu wanda ya san ko yana da rai ko ya mutu. Muna sa ran yana raye, amma babu tabbas. ‘Yan bindigan sun fada mana za su fito da shi idan an biya kudi.”

“Mun biya kudin amma ba ju daga gare su ba tun bayan lokacin da muka kai masu kudin.” – ‘Danuwansa.

A cewar wannan Bawan Allah, tun da aka kai wa ‘yan bindigar kudin fansa, babu wani wanda ya samu damar yin magana da mai martaba saboda rashin waya.

Zuwa yanzu ai an dawo da layukan sadarwa na waya a fadin jihar Zamfara, amma babu wata magana mai karfi da aka ji a kan batun Sarkin na kasar Bungudu.

A farkon makon nan ne aka ji cewa Gwamnatin Nasir El-Rufai ta amince da nadin Alkali Muhammad Inuwa Aminu a matsayin sabon Wazirin kasar Zazau.

Sakataren Masarautar Zazzau, Alhaji Barau Musa Aliyu ya aika wa sabon Wazirin takarda zuwa gidansa a Unguwan Juma, a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba, 2021.

Source: Legit

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN