Jerin yan siyasan Arewa 10 da ke kan gaba wajen neman kujerar shugaban Jam’iyyar PDP

An fara buga siyasa domin ganin an zabi sabon shugaban jam’iyyar PDP na kasa. This Day tace jiga-jigan Arewa na kokarin fitar da ‘dan takara daya.

Tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido sune ‘yan gaba-gaban wajen rike jam’iyyar adawar.

Jaridar tace Olusegun Obasanjo yana tare da Sule, shi kuma Mark ya samu goyon baya ne daga irinsu Janar Aliyu Gusau da wasu tsofaffin sojoji ‘Yan Arewa.

Daga cikin wadanda ake tunani suna sha’awar samun mukamin akwai tsofaffin gwamnoni; Dr. Muazu Babangida Aliyu, Ibrahim Idris da Ibrahim Shehu Shema.

Aliyu, Idris da Shema sun yi mulki a jihohinsu na Neja, Kogi da Katsina. Barista Shema ne kadai a cikinsu ya fito daga bangaren Arewa maso yammacin Najeriya.

Ana tunanin Mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Suleiman Nazif yana kwallafa rai a kujerar. Haka zalika Dr. Iyorchia Ayu, da Farfesa Jerry Gana.


Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom shi ne yake kokarin ganin kujerar ta fada hannun Iyorchia Ayu, wanda ya taba zama shugaban majalisar dattawa na kasa.

Wani wanda ake tunani za a gwabza da shi wajen zama shugaban jam’iyyar ta PDP shi ne tsohon gwamnan jihar Kaduna,anata Ahmad Muhammad Makarfi.

A ranar Lahadi, 10 ga watan Oktoba, 2021, Legit.ng Hausa samu labari cewa Dino Melaye zai nemi mukamin, ganin cewa za a fito da shugaban PDP ne daga Arewa.

Akwai yiwuwar yayin da aka fara saida fam a yanzu, a ji cewa masu neman kujerar sun kara yawa.

Ga jerin ‘yan takarar nan:

1. Sanata David Mark

2. Alhaji Sule Lamido

3. Dr. Muazu Babangida Aliyu

4. Ibrahim Idris

5. Ibrahim Shehu Shema.

6. Sanata Suleiman Nazif

7. Dr. Iyorchia Ayu,

8. Farfesa Jerry Gana.

9. Ahmad Makarfi

10. Dino Melaye

Dazu ne muka ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta lashe baki ɗaya kujerun da aka yi takara kansu a zaɓen kananan hukumomi na jihar Filato da aka gudanar.

Hukumar zaɓe ta PLASIEC, ta ce APC ta lashe kujerun shugabannin hukumomi 17 da kansiloli 235.

Source: Legit

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN