Jami'an Kwastam sun bude wuta kan jama'a a jihar Katsina


Rahotanni daga jihar Katsina sun tabbatar da cewa jami'an kwastam sun bindige mutum ɗaya a ƙaramar hukumar Mani.

Hukumar yan sanda reshen jihar ta bayyana cewa wanda aka harbe, Auwal Sani, 35, an harbe shi ne a kafarsa, inda daga baya aka kaishi asibiti domin kulawa da lafiyarsa.

Premium times ta rahoto cewa Lamarin ya faru ne lokacin da jami'an kwastam a cikin motar sintiri suka shiga ƙauyen Fadi Gurje dake ƙaramar hukumar Mani, jihar Katsina.

Shigarsu ƙauyen ke da wuya, sai jami'an na hukumar kwastam ta ƙasa suka bude wuta kan mai uwa da wabi, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Katsina, Gambo Isa, yace jami'ai sun dukufa bincike don gano masu hannu a lamarin daga cikin jami'an kwastam.

Isah ya ƙara da cewa kwamishinan yan sanda na jihar ya yi kira ga al'ummar yankin su kwantar da hankulansu.

Ya kuma roƙi mutanen dake zaune a yankunan da lamarin ya shafa su cigaba da harkokinsu na yau da kullum yayin da yan sanda ke bincike.

Kakakin yan sandan ya ƙara da cewa jami'an yan sanda na aiki kafaɗa-da-kafaɗa da kwastam domin warware matsalar.

Kwastam sun taba kashe mutum 10

Idan baku manta ba, a baya jami'an kwastam sun hallaka mutum 10 tare da jikkata wasu da dama yayin da direban motar sintiri yayi kan jama'a.

Legit.ng Hausa ta kawo muku cewa direban motar kwastam ɗin ya faɗa kan jama'a ne lokacin da suka biyo ɗan sumogal a ƙaramar hukumar Jibiya.

Legit hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN