Iyaye sun fara saida ‘ya ‘yan cikinsu saboda tsabar masifar talauci a kasar Afghanistan


Afghanistan - Kasar Afghanistan na fama da mummunan tsananin rayuwan a karkashin jagorancin kungiyar Taliban da ta karbi ragamar mulki. 

Wani rahoto da BBC News ta fitar ya bayyana cewa an samu iyayen da sun fara saida ‘ya ‘yan cikinsu domin su samu kudin ciyar da ragowar yaransu. 

‘Yar jaridar BBC, Yogita Limaye tayi hira da wasu mutane a Herat da suka saida karamar diyarsu a kan $500 saboda su ciyar da sauran 'ya 'yan da suka haifa. 

Wanda ya saye yarinyar ya bayyana cewa ya yi haka ne domin ya kula da ita har ta girma, sai ta auri ‘dansa. Sai daga baya ne zai karbi wannan yarinyar. 

Mutumin ya biya $250, wanda zai ciyar da iyalin na wasu ‘yan watanni, daga baya zai cika sauran kudin idan ya zo karbar jaririn lokacin da ta koyi magana. 

Yarana za su mutu, dole na saida ta ... “Sauran ‘ya ‘yana suna mutuwa da yunuwa, saboda haka dole mu ka saida ‘ya ta. Ya za ayi ba zan ji takaici ba? ‘Yar ciki na ce. Ina ma ban saida ta ba.” 

“Yunwa na neman kashe mu, ba mu da fulawa, ba mu da mai a gida, babu komai. ‘Diya ta ba ta san ya za ta kasane nan gaba ba.” – inji Mahaifiyar ‘diyar. Wannan mata tace ba ta san ya ‘diyar ta za ta ji idan ta ji labari wata rana ba, amma babu yadda ta iya. 

Mahaifin yaran yana yawon daukar bola ne, yanzu babu aiki don haka babu kudi. Akwai wata mai goge-goge da ta saida ‘yar ta, aka yafe mata bashin $550. 

Yara akalla takwas suka mutu kwanan nan a birnin Kabul saboda yunuwa. Lamarin ya kai har wasu suna cewa za su kashe kansu, su huta da rayuwar Duniya. 

Taliban sun kawo sababbin tsare-tsare Hakan na zuwa ne bayan sojojin Amurka sun fice daga Afghanistan, an bar kungiyar Taliban da iko. 

Kwanaki aka yi shamaki tsakanin ‘yan mata da maza a makarantun kasar Afghanistan. Yanzu babu dama mace ta hadu da wani namiji a cikin makarantar boko. 

Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN