ICPC: Yadda muka kwato gidaje 301 daga jami'an gwamnati 2 a Abuja


Hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta, ICPC ta ce ta samo gidaje 301 da aka wawuri kudi aka siya daga jami'an gwamnati a babban birnin tarayya na Abuja, TheCable ta wallafa. 

Bolaji Owasanoye, shugaban hukumar ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wani taron da kwamitin majalisar wakilai na wucin-gadi suka shirya kan ayyukan masu siyar da filaye da gidaje a babban birnin tarayya. 

A yayin jawabi a taron, Owasanoye ya ce hukumar ta samu korafi daban-daban kan ayyukan handama. Ya ce rashin rijistar gidaje da filaye a babban birnin tarayya yadda ya dace ne ya janyo rashawa a bangaren, TheCable ta wallafa. 

Duk da ba mu da jimillar yawan matsalolin da suka shafi filaye, mun samu korafi daga masu ruwa da tsaki a harkar gidajen, masu siya da kuma jama'ar gari kan yadda dillalan ke cuta a ciki da wajen Abuja," 

yace. “Wadannan korafe-korafen suna da yawa. Sun hada da sa hannun bogi, siyar da fili ga mutane da yawa, bada fili ba tare da amincewar minista ba, kwace filaye ba tare da bin hanyar da ya dace ba da sauran kalubale makamantan hakan. 

“Sai kuwa jami'an gwamnati masu handamar kudaden su na amfani da harkar wurin boye dukiyar sata da boye kudade. Su kan yi amfani da harkar wurin siyan filayen suna adanawa da kudin sata. 

"Hukumar ta kwato gidaje 241 daga jami'in gwamnati inda ta sake kwato wasu gidaje 60 daga wani jami'in," yace. Hakazalika, Daniel Esei, mataimakin daraktan EFCC ya ce ya dace a karfafa hukumar ta dinga daukan mataki kan wadanda ta kama da boye kudaden haram. EFCC ta sako tsohon shugaban majalisar dattawa bayan kwashe kwana 2 a hannun ta 

Legit Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN