Masu yi wa kasa hidima guda biyu da yan bindigan suka sace a Zamfara kan hanyarsu ta zuwa jihar Kebbi sun sami yanci.
Shafin isyaku.com ya samo cewa Jimin Geoffrey, mai taimaka wa Gwamnan jihar Benue kan harkar kafofin sada zumunta ya sanar da haka a wata Takarda da ya fitar ranar Laraba 27 ga watan Oktoba.
Ya ce an saki yan NYSC ne bayan kokarin shiga tsakani da Gwamnatin jihar Benue ta yi tare da hadin gwiwa da shugabannin kamfanin motocin zirga zirga na Benue Multi links da iyayen wadanda aka sace.
Jennifer Awashima Iorliam da Josephⁿ0 Zakaa yan NYSC ne da ke kan hanyarsu ta zuwa jihar Kebbi wajen aikin yi wa kasa hidima. Sauran sun hada da Sedoo Kondo wacce ke karatu a Jami'ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto, da Ruth Sesuur Tsokar wacce ke kan hanyarta domin ziyarar dan uwanta a jihar Kebbi, da wasu yan uwan juna guda biyu, Muhammadu Saminu da Safiam Muhammadu wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa jihar Sokoto suna cikin motar kamfanin motocin zirga zirga na jihar Benue ne Multi Links ko da lamarin ya faru.
Sanarwar ta ce Yan bindigan sun saki matasan ne da karfe 6 na yammacin ranar Talata 26 ga watan Oktoba. Sai dai Geofrey bai ambaci ko kars bayani ko an biya kudin fansa kafin a sako matasan ba.
Rubuta ra ayin ka