Type Here to Get Search Results !

Girma ya fadi: An kama Malamin addini bayan ya aikata wa wata yarinya mugun aiki, duba abin da ya faru


Rundunar NSCDC na jihar Oyo ta gurfanar da wani malamin addnini mai suna Alfa Olayiwola Rasak a gaban Kotu bisa tuhumar sa da yi wa yarinya yar shekara 15 fyade.

Shafin isyaku.com  ya samo cewa wata takardar sanarwa da ta futo daga Kwamandan rundunar ta jihar Oyo Mr. Adaralewa Michael ya tabbatar da zancen. Ya ce an gurfanar da Malamin ne a gaban Kotu bayan ya aikata laifin.

Ya ce wanda aka kama, mazauni gida mai lamba No S6/387 a kan titin Oke Oluokun Kudeti da ke Birnin Ibadan ya sha aikata wa yarinyar fyade har tsawon shekara hudu da suka gabata.

Shugaban Koktun iyali Chief Magistrate S. H. Adebisi, da ke lamba 1 Iyaganku a birnin Ibadan, bayan sauraron kara da aka shigar kan Malamin, ya tasa keyarsa zuwa Kurkuku har ranar 8 ga watan Nuwamba 2021 domin ci gaba da shari'ar.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies