Duba yadda magidanci ya sheƙe abokinsa bayan ya yi mafarkin ya kwanta da matarsa


Wani magidanci mai shekaru 45 mai suna Kwadwo Adusei wanda aka fi sani da Desco, ya shiga hannun jami'an tsaro kan halaka abokinsa a Wawaase da ke Afigya Kwabre ta kudu a yankin Ashanti na kasar Ghana.

Wanda ake zargin ya sheke abokinsa ne bayan ya yi mafarkin cewa ya kwanta da matarsa, shafin LIB suka wallafa.

An gano cewa ya yaudari marigayin mai shekaru 48 mai suna Kwesi Banahene zuwa daji inda ya soka masa wuka sau da yawa a sassan jikinsa.

Daga bisani an tsinci gawar mamacin a daji bayan an tura masu nema neman shi sakamakon batan da ya yi na kwanaki.

Makashin an gano ya yi yunkurin sheke kakansa bayan kashe abokinsa da yayi. Daga bisani ya zargi kakansa da sace masa mazantaka, lamarin da yasa ya kasa haihuwa.

Kakaknsa ya tsallake farmakin kuma a halin yanzu ya na asbiti Ankaase inda ake kula da shi.

Desco ya sanar da manema labarai cewa, shi sau da yawa mafarkinsa na zama gaskiya kuma ba zai iya jira ya ga wannan ya zama gaskiya ba, wanda hakan yasa ya yi hanzarin daukar mataki.

Legit Hausa

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari