Duba dalilin da ya sa Kotu ta dakatar da sabon Sarkin Kontagora


Wata babbar kotu a Minna babban birnin jihar Neja a arewacin Najeriya ta tuɓe sabon Sarkin Kontgora Muhammad Barau wanda gwamnan jihar ya naɗa a makon da ya gabata.

Alkalin Kotun Justice Abdullahi Mikailu ya umarci sabon sarkin ya daina kiran kansa a matsayin Sarkin Sudan na Kontagora.

Da yake yi wa manema labarai karin bayani jim kadan bayan yanke hukuncin, lauyan wadanda suka shigar da kara Barista Yusha'u Mamman, ya ce tun farko mutane uku suka shigar karar, da suka hadar da kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, da kwamishinan shari'a da kuma sarkin da kotun ta dakatar a yanzu.

Tun farko wasu mutane 15 da suka nemi sarautar ne suka shigar da kara a gaban kotun, suna kalubalantar matakan da aka bi wajen zabar Muhammadu Barau a matsayin sarkin na Kontagora.

Hukuncin da kotun ta yanke a yanzu na nufin an dakatar da Muhammadu Barau daga amsa sunan sarkin Kontagora, har zuwa lokacin sauraro da tabbatar da kudirin waɗanda suka shigar da ƙarar.

Alƙalin kotun yanzu ya dage sauraren ƙarar har zuwa ranar 20 ga watan Oktoban bana.

A makon da ya gabata ne gwamnatin Neja ta sanar da Mohammed Barau Kontagora a matsayin Sarkin Kontagora na bakwai, cikin wata sanarwa daga kwamishinan kula kananan hukumomi da masarautun jihar.

Kwamishinan ƙananan hukumomi da ci gaban al'ummomi da masarautun gargajiya Emmanuel Umar, ya ce an zaɓi sabon Sarkin Sudan na Kontagoran ne a ranar Lahadi 19 ga watan Satumban 2021, kuma manyan masu zaɓar sarki na masarautar ne suka yi hakan.

Kwamishinan ya ce: "Masu zabar sarkin sun tabbatar wa gwamna cewa sun yi zaɓen ne ta hanyar bin dokokin al'adu na Masarautar Kontagora, kuma sun yanke hukuncin ne bisa fahimtarsu ba tare da tsoma bakin wani daga waje ba."

Sanarwar ta ce " a don haka kamar yadda doka ta tanadar wa gwamna, ya amince da matakin na su tare da tabbatar da Mohammed Barau Kontagora a matsayin Sarkin Sudan na bakwai."

Tun rasuwar Sarkin Sudan na Kwantagora, Alhaji Saidu Umaru Namaska a ranar 9 ga watan Satumba, batun wanda zai gaje shi ke jan hankali a jihar Neja.

Sarkin Sudan na Kwantagora wanda fitaccen sarki ne a cikin masarautun arewacin Najeriya, ya rasu ne yana da shekara 84.

Sarki Saidu Umaru Namaska ya shafe shekara 47 a kan karagar Sarautar Kontagora.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN