Duba dalilin da ya sa ake yawan samun ɗaukewar shafukan sada zumunta


Ba na tunanin Mark Zuckerberg na karanta sakonnin da a ke wallafawa a shafukan Facebook.

Da a ce zai karanta, to zai dauke shi akalla kwanaki 145 ba tare da bacci ba kafin ya iya karance tarin martanin da a ka yi masa, a lokacin da ya ba da hakuri bayan daukewar shafukan Facebook da WhatsApp da kuma Instagram.

" Ina ba ku hakuri da tangardar da aka samu yau'' a cewar mamallakin na Facebook bayan da shafukan Facebook da WhatsApp da Instagram suka dauke.

Facebook ya ta'allaka matsalar da wasu gyare-gyare da ya saba yi. To amma a wannan karon injiniyoyinsa sun barkata tsarin cikin kuskure wanda ya sa intanet din wadannan shafuka suka dauke a fadin duniya.

Akalla mutun 827,000 ne su ka yi wa Mr Zuckerberg martani a lokacin da ya bada hakuri.

''Wannan abu ya yi muni, dole na yi magana da iyalina.'' Inji wani ba'italiye.

Shi kuma wani mutun daga Namibia sai ya rubuta cewa '' Na je na kai gyaran wayata tunanin cewa ta samu matsala ne.''

Wani dan kasuwa daga Najeriya ya nuna rashin gamsuwa da abin da ya faru, inda ya rubuta cewa '' ba zai yiyu ba ku ce komai ya dauke a lokacin guda.''

Har ma ta kai ga wani daga Indiya yana bukatar a biya shi diyya kan tsayawar wadannan shafuka.

A yanzu dai abin da ya fito fili game da tsayawar wadannan shafuka shine irin yadda biliyoyi a fadin duniya suka dogara ga wadannan shafuka, ba wai don nishadi ba kawai hadda gudanar da cinakayya.

Sana'o'i da dama sun dogara sosai ga shafukan Facebook da WhatsApp da kuma Instagram don hulda da kwastomominsu

Wani abin kuma da aka fahimta shi ne ga alama za a cigaba da samun daukewar wadannan shafuka akai-akai kamar yadda masana suka yi hasashe.

"Abin da muka fahimta a tsawon shekaru shine karuwar dogaro da shafukan sada zumunta da kuma kamfanonin fasaha wurin aiki da intanet, a cewar Luke Deryckx, ma'aikaci a kamfanin fasaha na Down Detector.

"A duk lokacin da dayansu ya samu matsala ya kan shafi daruruwan dubban shafuka, misali Facebook wanda za ka iya amfani da shi wurin bude shafuka da dama.

"Saboda haka da zarar shafukan suka dauke ba zato ba tsammani sai mu fara kallon juna da tunanin cewa ta ina za mu fara." Inji Deryckx.

Aikin Mista Deryckx da abokan aikinsa su ke yi a Down Detector shine sa ido don tabbatar da cewa shafukan intanet na aiki ba bu tangarda.

Kuma a yanzu sun lura cewa ana samun daukewar intanet a kai-a kai.

Luke Deryckx ya kara da cewa " a duk lokacin da Facebook ya samu matsala hakan na mummunan tasiri ga intanet da kuma tattalin arziki. Kuma daruruwan miliyoyi za su zauna jiran wasu tsiraru a birnin California su magance wannan matsala. Wannan abu ne da ke neman zama ruwan dare a yan shekarun da suka gabata."

Wani zargi kuma da ba zai gushe a zukatan masu amfani da shafukan ba shi ne cewa matsalar ta faru ne saboda hare-haren intanet da ake kai wa, musamman daukewar shafukan na baya bayannan.

To amma masana sun ce a lokuta da dama matsalar ta ma'aikata ce da kuma tsufan da wasu kayan aiki suka yi.

Farfesan kimiyyar intanet Bill Buchanan ya jaddada wannan batu, inda ya ce " wasu kayan aiki fasaha da a ke amfani da su sukan yi wa kwamfutoci nauyi sosai wanda hakan yake sa su dakata daga aiki".

A kan haka ya kara da cewa " akwai bukatar a gudanar da sauye-sauye da za su inganta intanet din da shafukan ke amfani da ita."

Masana dai na ganin bai kamata a rika yi wa wannan matsala kallon karama, lura da yadda take aukuwa nan take.

Masana sun ce a lokuta da dama matsalar ta ma'aikata ce da kuma tsufan da wasu kayan aiki suka yi

Hakama Farfesa Buchanan na ganin ya kamata a kara maida hankali kan inganta rumbunan ajiyar bayanai, idan ba haka ba kuma akwai yiyuwar a ci gaba da samun daukewar intanet a wadannan shafuka a nan gaba.

Hujjar da Farfesan ya kafa ita ce intanet da ake amfani da ita a duniya kusan daga wuri daya ake rabata. Bugu da kari rumbun ajiyar bayanan intanet din sun yi nauyi wanda hakan yake sa da an samu matsala karama sai ta shafi kowa da kowa.

Kamar yadda mujallar Forbes ta wallafa, Facebook ya tafka asarar dala miliyan 66 a tsawon awa shida da aka shafe ba a yi amfani da wadannan shafuka ba.

Masana na ganin irin wannan asara za ta sa jiga-jigai a kamfanoni da dama su mayar da hankali wurin ganin irin haka ba ta sake faruwa ba.

"Sun rasa makudan kudade a ranar a cewar Mr Deryckx, " kuma an rasa kwastamomi masu yawa sosai, saboda haka nake ganin cewa masu ruwa da tsaki a wannan harka za su yi duk mai yiyuwa su ga cewa hakan ba ta sake faruwa ba".

BBC Hausa

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN