Duba abin da yan Luwadi da Madigo suka yi a Afghanistan sakamakon mulkin Taliban


Wani rukunin ƴan madigo da luwadi masu gudun hijira daga Afghanistan sun isa Biritaniya.

Mutanen 29 - wadanda suka haɗa da ɗalibai da masu fafutukar kare haƙƙin masu maɗigo da luwadi da ake kira LGBT su ne rukunin farko da aka kai Birtaniyya tun bayan kawo ƙarshen tashin jiragen sama a Kabul bayan kwace iko da Taliban ta yi.

Gwamnatin Birtaniya da ƙungiyoyin agaji na ƙasar da Canada ne suka taimaka musu ficewa daga Afghanistan.

Sakataren harkokin waje, Liz Truss, ta ce Birtaniyya za ta ci gaba da kare ƴancin dukkanin mutane su rayuwa yadda suke so.

BBC Hausa
Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN