Duba abin da ke faruwa da Musulmai bakaken fata kafin su sami masoya a kasar Britaniya


Akwai mutanen da ke gaya min cewa gaskiya kana da kyau, ka dace da 'yar uwata amma kuma kai bakar fata ne. Sai na ji abin ... kamar
.''

Ga Kha'llum Shabbaz, jinsinsa ya haifar masa da kalubale wajen samun masoyiya a matsayinsa na Musulmi a Birtaniya.

"A bangare daya idan ana maganar addini ne, kai Musulmi ne, amma kuma bakar fata.Amma kuma ta daya bangaren, idan aka zo batun al'ada, sai a ce kai bakar fata ne ko kuma Musulmi. To ta ina za ka yi galaba?" in ji Kha'llum mai shekara 28 a tattaunawarsa da shirin Inglishi na tashar BBC ta Radio 1 mai suna Newsbeat.

Oktoba wata ne na waiwayar wani tarihi na bakaken fata, kuma yana ganin za a iya mantawa da bakaken fata Musulmai a bukukuwa da tarukan lokacin.

Kha'llum

ASALIN HOTON,KHA'LLUM

Bayanan hoto,

An haifi Kha'llum Musulmi, amma yana ganin mutane na masa kallo na daban saboda shi bakar fata ne

Kha'llum, wanda yake daga birnin Birmingham, na Ingila, ya ji alamu a jikinsa lokacin da zai je ya gana da iyaye da 'yan uwan wata budurwa da yake kauna.

Irin abubuwan da ya gamu da su, sun sa har ya fara tunanin ko ma dai kawai ya shiga matar da ba ta jinsinsa ba, wato wadda ba bakar fata ba.

"Kai sai ma dai na ji cewa ko dai na dan dakata da maganar auren nan ne, sai nan gaba," in ji shi

Bayanan bidiyo,

..

Ba shi kadai ba ne ya samu kansa a wannan hali ba.

Wani bincike da daya daga cikin manyan shafukan hada masoya Musulmi, da ake kira Muzmatch ya yi a kan masu amfani da shi su 400, ya gano cewa kashi 74 cikin dari na mambobinsa bakaken fata, suna ganin jinsinsu ya shafi alakarsu da wadanda suka samu.

An fito da batutuwa kamar su wariya da launin fata da daukar wani jinsi da cewa ya fi kyau, inda wasu bakaken fata a shafin suke ganin ba a la'akari da su sosai a irin wadannan shafuka.

Ga Kaya mai shekara 31, ita a ko da yaushe tana danganta kanta a kan wadannan batutuwa a matsayinta na bakar fata Musulma a shafukan hada masoya.

"Ba wai a ko da yaushe ana yin abin da niyya ba ne, amma na fahimci cewa akwai maza da yawa da za ka ji suna gaya maka maganganu kamar su ce, 'kai ! Gaskiya kin yi' su ce za su so a ce sun auri mata bakar fata, su haifi 'ya'ya masu launin jinsin farar fata da bakar fata''

''Ana kokarin boye abin ne kawai, a ga kamar babu shi, amma a gaskiya ba wani abin alheri ne ga kowa ba."

Tana ganin akwai mutanen da a al'adarsu suke nuna wa bakaken fata Musulmi wariya da bambanci.

"Akwai lokacin da wani ya taba gaya min cewa shi ya fi son a ce ya auri matar da take daga jinsinsa, tun daga nan bai kara min magana ba. Kowa yana da damar ya zabi abin da yake so, amma abin da ciwo."

'Kasancewa a matsayin Musulmi'

Abubuwan da Kha'llum da Kaya suka hadu da su ko aka yi musu a harkar neman abokan aure na nuni da irin yadda al'amura suke ga Musulmi bakaken fata a cikin al'umma.

Kha'llum, wanda aka haife shi Musulmi, ya ce mutane "kusan suna kallona wani daban", kuma kusan ko da yaushe sai a rika tambayarshi lokacin da ya Musulunta.

Zainab Hassan, kwararriyar mai yi wa mata kwalliya tana jin cewa, "dole ne sai ka nuna a aikace kafin a san kai Musulmi ne" a matsayinka na bakar fata, wanda kuma ba haka abin yake ba a kan wadanda ba bakar fata ba.

"Wurin da kake yana da tasiri sosai a kan wannan, saboda lokacin da nake Najeriya, kasancewata bakar fata kuma Musulma, wannan ba ma wani abu ba ne, abu ne da kusan kowa yake haka. Ina ganin kamar tun da na fara sanya hijabina, a fili take cewa ni Musulma ce," in ji Zainab mai shekara 27, daga Manchester.

Zainab Hassan

ASALIN HOTON,ZAINAB HASSAN

Bayanan hoto,

Zainab ta ce: "Ina ganin akwai yanayin da dan cin zarafi da takurawar da ake yi maka za su fara shafarka"

Zainab ta ce akwai akidar kyamar bakaken fata a cikin wasu al'ummomin Musulmi.

"Idan ka yi wani abu ba daidai ba, kamar dai a ce ne, 'ai bakar Musulma ce', ba abin mamaki ba ne."

Kaya wadda ta Musulunta ne, tana jin takaicin yadda ake nuna wannan wariya, tana mai cewa yadda ta rungumi addinin kuma take yinsa da gaskiya ko da wadanda aka haifa ma a cikinsa ba za a ce sun fi ta ba.

Ta kara da cewa, "Akwai wasu matsalolin wadanda daga cikin mutane ko kabilu suke fitowa. Wadanda abubuwa da wasu mutane da iyalai suke dora wa kai, wadanda ba addini ne ya bukaci hakan ba, al'ada ce kawai."

Ta ce dangin tsohon mijinta ne suka haddasa mutuwar aurenta saboda, ''ba su ji dadin cewa ya auri bakar fata ba, wanda kuma ni ba zan iya boye kaina cewa ni ba bakar fata ba ce".

Zainab Hassan

ASALIN HOTON,ZAINAB HASSAN

Bayanan hoto,

Zainab ta taba shiga yanayin da ita kadai ce bakar fata a wani masallaci, tana jin kamar saniyar ware, ''ina jin kawai ban dace da wurin ba"

Tun bayan zanga-zangar kishin bakar fata da ta karade duniya ( Black Lives Matter) bayan kisan George Floyd, Zainab na ganin an dan samu sauyi.

"Ina ganin gaba dayan zanga-zangar, hatta lokacin da ta zo, kasancewata zaune a gida tare da iyayena, ta kawo sauyi."

"Ba za a yi saurin cewa komai ya sauya ba, amma daga irin maganganun da nake gani, hatta shafukan da nake bi na intanet, ina ganin a yanzu ba a nuna wa bakaken fata Musulmi wariya sosai.''

Domin samun sauyi yadda ya kamata, Kha'llum na ganin ya kamata bakaken fata Musulmi ya kasance sun samu dama ta su.

Ya kara da cewa, "ya kamata kowa ya ji cewa ana damawa da shi, domin abu ne me kyau ka ji cewa ba a mayar da kai saniyar ware ba."

Bayanan bidiyo,

..

Kaya na ganin ya kamata a samu karin wakilici domin ganin ana damawa a dukkanin harkoki da bakaken fata Musulmi.

"Ba za ka ga bakaken fata Musulmi da yawa suna jagoranci a aji ba, ko a matsayin limamai ba."

"Idan ba ka ga wanda yake mai kamanni irin naka ba, a ko da yaushe za ka ji kamar an mayar da kai saniyar ware a cikin al'umma."

'Dukkanmu za mu iya rayuwa tare'

Zainab tana ganin ya kamata kungiyoyin Musulmi su tashi tsaye haikan, amma kuma duk da haka alhaki ne da ya rataya a wuyan al'umma.

Kuma tana ganin samar da wani wuri da za a ce na bakar fata Muslmi ne kawai ba zai haifar da wani bambanci ko rarrabuwar kai ba.

Ta ce, "idan a baya kana daukar cewa an hana ka wannan dama ko wuri, to yana da kyau idan aka ce a yanzu an samar da wannan wuri."

Ta kara da cewa : "Dukkaninmu za mu iya rayuwa tare ba tare da an raba wani da, al'ada ko jinsinsa ba. Ba lalle sai mun rasa jinsinmu na kasancewa bakar fata ba, ko kasancewarmu Musulmai ba."

BBC Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN